Aminiya:
2025-04-12@21:13:54 GMT

An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe

Published: 10th, April 2025 GMT

Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da miyagun laifuka, inda ta cafke wasu fitattun mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane.

Waɗanda aka kama sun haɗa da: Babaro Baushe mai kimanin shekara 40 da Umaru Dau’a, mai kimanin shekara 25 da suka fito daga ƙauyen Askuwari a ƙaramar hukumar Tarmuwa a ranar 9 ga Afrilu, 2025.

Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi

A takardar sanarwar da kakakin rundunar ‘Yan sandan Yobe, SP Dungus Abdulkareem ya fitar ya ce, hedikwatar ’yan sanda reshen Dapchi da misalin ƙarfe 0500hrs, 9 ga Afrilu, 2025, ta cafke waɗanda ake zargin, ’yan ƙungiyar da suka ƙware wajen yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kuma neman barace-barace, suna gudanar da ayyukansu a ƙananan hukumomin Dapchi da Tarmuwa.

An dai alaƙanta waɗanda ake zargin da laifuka da dama da suka haɗa da: A ranar 21 ga Nuwamba, 2024, masu garkuwar sun kai hari ƙauyen Badegana da kuma kai hari gidan wani da aka kashe, wanda ya yi sanadin rasa rai.

A ranar 10 ga Maris, 2025, waɗanda ake zargin sun karɓe N250,000 da ƙarfi daga Mudi Ibrahim na ƙauyen Askuwari, ƙaramar hukumar Tarmuwa, bayan sun yi barazanar sace shi ko kuma su kashe shi.

Waɗannan mutane sun amsa laifukan da suka aikata, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a sashin bincike na jihar (SID).

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado  ya ba da umarnin ci gaba da ƙoƙarin kama wasu ’yan ƙungiyar kuma ya buƙaci al’umma da su bayar da sahihan bayanai don taimakawa wajen gudanar da bincike.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Tarmuwa yan sandan

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi

Wasu mahara sun harbe wasu mata biyu har lahira tare da banka musu wuta a gonakinsu da ke ƙauyen Okete a Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi.

Lamarin ya faru ne a lokacin da kowacce daga cikin matan biyu ke tsaka da kula gonarta.

An ce maharan sun yi musu ruwan harsasai baya wata taƙaddama da ta ɓarke, sannan suka tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Wani mazaunin yankin ya ce, “Muna cikin juyayi tun da muka samu labarin harin da aka kai wa ’ya’yanmu mata a gona. Sun je gonakinsu ne domin su kula da su a ranar Laraba, abin takaici sai wata ta ƙaddamanta ɓarke, kuma maharan, waɗanda ake zargin makiyaya ne, suka harbe su har lahira.

“Mun yi tunanin za mu ɗauko su da rai ne lokacin da muka samu labarin a ranar Laraba, amma sai muka iske gawarwakinsu an yi musu ruwan harsasai da kuma ƙuna a jikinsu.”

Cutar Kwastomomi: NERC ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar N628m ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano
  • Tawagogin gwamnatin Kongo da kungiyar M23 sun isa  Doha domin tattaunawa
  • ’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi
  • Sabon Kwamishinan Na Kwara Ya Sha Alwashin Dakile Laifuka
  • Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe
  • Iran Da Armenia Suna Fara Atisayen Hadin Giwa Don Karfafa Tsaron   Kan Iyakar Kasashen Biyu
  • Yadda masu safarar ɗan Adam ke yaudarar mutane ta intanet
  • Ruwa Ya Ci Rayukan Mata Biyu A Kano
  • Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Bayan Kashe Ɗan Bindiga A Katsina