Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe
Published: 10th, April 2025 GMT
Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta ce, ta warware rigingimu 565 a cikin watanni 12 da suka gabata a jihar.
Wannan hukuma dai gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya kafa ta a watan Maris, 2024 a wani ɓangare na ƙoƙarin magance munanan ɗabi’u a jihar.
Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji An kama masu garkuwa da mutane biyu a YobeShugaban Hukumar ta Hisbah, Dakta Yahuza Hamza Abubakar, ya ce matsalolin da aka warware sun haɗa da batutuwan da suka shafi: Harkar iyali da kasuwanci da gado da kuma basussuka.
Sauran matsalolin da hukumar ta Hisbah ke warwarewa sun haɗa da: Matsalolin da haddasa rikicin manoma da makiyaya da kuma rashin biyan kuɗin haya.
A cewarsa, an warware akasarin shari’ar ta hanyar sulhu da fahimtar juna.
Dokta Hamza ya ce, jami’an hukumar sun kuma ƙwace kwalayen barasa guda 56 da kuma 18 na sinadaran fosters na methylene chloride chemical (Madarar Sukurdai) a faɗin jihar.
Ya ce, addinin Musulunci da dokar da ta kafa hukumar a shekarar 2024 ta haramta sayar da barasa da sauran kayan maye a jihar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ruwa Ya Ci Rayukan Mata Biyu A Kano
Mazauna karamar hukumar Gezawa ta Kano sun shiga cikin tashin hankali da makoki sakamakon nutsewar wasu mata biyu a cikin wani tafki.
Rahotanni sun nuna cewa matan (an sakaya sunansu) sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke wanka a kogi bayan sun dawo daga aiki a wata masana’antar sarrafa hibiscus.
A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusif Abdullahi Gezawa hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga ‘yan banga da ke yankin tare da bayyana cewa “Yan uwan matan biyu ne suka kai rahoton lamarin ga dan banga”
Ya yi nuni da cewa, nan take aka tura tawagar masu aikin ceto zuwa wurin, inda suka yi nasarar zakulo gawarwakin su a sume, daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu.
Saminu ya bayyana cewa an mika gawarwakin ga wani dan sanda Musa Garba na sashin ‘yan sanda na Gezawa.
Ya shawarci jama’a da su daina zuwa kusa da kogi domin gujewa abubuwan da ba a zata ba.
KHADIJAH ALIYU