Aminiya:
2025-04-12@20:59:34 GMT

Gwamnati ta gargaɗi jihohi 30 kan ambaliyar ruwa

Published: 11th, April 2025 GMT

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi hasashen za a yi ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Jihohin da ake fargabar fama da ambaliyar ruwan sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Riɓers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma babban birnin tarayya.

An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi

Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev, a ranar Alhamis, ya ce za a fuskanci ambaliyar ruwa a gaɓar teku da koguna a wasu sassan yankunan Kudu maso Kudu na ƙasar, sakamakon ƙaruwar ruwan teku.

Daga cikin waɗannan jahohin akwai: Bayelsa, Cross Riɓer, Delta, da Ribas yayin da Akwa-Ibom da Edo suka faza cikin jihohin da ake fargabar yin ambaliyar.

Utseɓ ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da taron shekara na 2025 (AFO) na hasashen ambaliyar ruwa da Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) ta gudanar a Abuja.

A taron na 2025 na Shekara-shekara kan Ambaliyar Ruwa (AFO) an raba su zuwa sassa uku don magance ƙalubalen iftila’in ambaliya da ba da bayanai don rage faruwar hakan, musamman a cikin unguwannin jama’a masu rauni.

Ministan ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta kasance ɗaya daga cikin ibtila’o’in da suka fi yin ɓarna a Nijeriya tare da sauyin yanayi da ke ƙara ƙaimi da tsanani.

Ya bayyana cewa unguwanni 1,249 a ƙananan hukumomi 176  a faɗin jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja sun faɗa cikin yankunan da ake fama da ambaliyar ruwa a wannan shekarar, yayin da ƙarin unguwanni 2,187 a ƙananan hukumomi 293 ke fuskantar haɗarin ambaliya. Muhimman wuraren da ke da haɗarin sun haɗa da Abia, Benue, Lagos, Bayelsa, Riɓers, Jigawa, da dai sauransu.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Adamawa Akwa Ibom Anambra Bayelsa Jigawa Kwara Nasarawa Taraba Zamfara ambaliyar ruwa

এছাড়াও পড়ুন:

Masarautar Kauru Ta Bayyana Rashin Sha’awarta Kan Shiga Sabuwar Jihar Gurara

Wata kungiya mai zaman kanta da ke dauke da sunan Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa ‘yan jarida a Zariya.

A cewar Malam Mukhtar, ikirarin da wasu ke yi musamman daga yankin Kudancin Kaduna na cewa Masarautar Kauru na son shiga cikin Jihar Gurara ba gaskiya ba ne kuma yana bata suna.

“Mutanen Masarautar Kauru ba su da hannu a wannan yunkuri. Muna alfahari da kasancewarmu a cikin Jihar Kaduna, musamman saboda alakar tarihi, al’adu da zamantakewa da muke da ita da Masarautar Zazzau,” in ji shi.

Ya ci gaba da bayyana cewa Masarautar Kauru da Masarautar Zazzau na da alaka mai karfi ta fuskar kima da dabi’u da aka gada tun zamanin da.

Yayin da yake karin bayani kan dangantakar zamantakewa da ta tarihi, Malam Mukhtar ya bayyana cewa:

“Daga auratayya, zuwa hanyoyin kasuwanci, bukukuwa da tsarin shugabanci na gargajiya, dukkanmu muna da zumunci da mu’amala da jama’ar Zazzau. Kokarin cire mu daga wannan tsari da saka mu a wani sabon tsari ba zai haifar da alheri ba.”

Ya jaddada cewa Masarautar Kauru “ta yanke shawara a fili” cewa tana so ta ci gaba da kasancewa a cikin sabon tsarin Jihar Kaduna da ake shirin kafawa, tare da kin amincewa da duk wani yunkuri na saka ta cikin Jihar Gurara.

A karshe, Shugaban KECI ya bukaci masu rajin kafa Jihar Gurara, musamman daga Kudancin Kaduna, da su daina kokarin saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin jihar, yana mai bukatar a girmama ra’ayin jama’ar yankin.

Cov/Jibirin Zaria

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis
  • Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?
  • ‘Tell Your Papa’: NBC ta haramta amfani da waƙar da ke sukar Tinubu
  • Rayuwar ‘Yan Arewa Na Cikin Hadari, Yayin Da Gurbataccen Gishiri Ya Fantsama A Kasuwanni
  • Masarautar Kauru Ta Bayyana Rashin Sha’awarta Kan Shiga Sabuwar Jihar Gurara
  • Sudan Ta Kai Karar HDL A Gaban Kotun Kasa Da Kasa Ta MDD
  • Za a mayar da tubabbun ’Yan Boko Haram cikin al’umma – Gwamna Buni
  • Ruwa Ya Ci Rayukan Mata Biyu A Kano
  • An Sace Dalibin Jami’ar Tarayya Birnin Kebbi