Cutar Kwastomomi: NERC ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar N628m
Published: 11th, April 2025 GMT
Hukumar Kula Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar naira miliyan 628 kan laifin karɓar kuɗin wuta fiye da kima daga hannun kwastomomi marasa mita.
Hukumar ta kuma ba wa kamfanonin rarraba lantarkin da hakan ta shafa wa’adin ranar 15 ga watan Mayu, 2025, sun tabbatar sun biya kwastomomin da suka canza fiye da kima, ta hanyar ba su wuta daidai da abin da suka ƙware su.
NERC ta bayyana cewa ɗaukar wannan mataki ya zama dole saboda kamfanonin sun yi kunnen ƙashi bayan umarnin da ta ba su, wanda ya ƙayyade kuɗin da su caji kwastomomi da ba su da mita.
Ta ce waɗanda aka ci tarar sun haɗa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (Kaduna Electric) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) da Kamfanin Rarraba Lantarki na Abuja (AEDC), Kamfanin Rarraba Lantarki na Jos da kuma Kamfanin Rarraba Lantarki na Yola.
Sauran su ne Kamfanin Rarraba Lantarki na Legas da takwarorinsa na Enugu da kuma Ikeja.
Sanarwar da Hukumar NERC ta fitar ta ce wannan tarar ta shafi kamfanonin guda takwas ne daga watan Yuli zuwa Satumbar shekarar 2024.
Ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna kamfanonin sun yi watsi da umarnin nata da ya ƙayyade cazar kwastomomi marasa mita da ke kan layin lantarki guda a duk wata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwastomomi Lantarki marasa mita
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Karamar Hukumar Maigatari Sun Bukaci Gwamnatin Jigawa Ta Gina Musu Hanyoyi
Al’ummar Karamar Hukumar Maigatari sun yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta taimaka wajen gina hanyoyin da za su hada garuruwansu.
Wani mazaunin yankin, Malam Ali A. Bulama Turbus, wanda ya wakilci al’ummomin yayin da yake magana da Rediyon Najeriya a Maigatari, ya jaddada muhimmancin aikin gina hanyar.
Ya bayyana cewa samar da hanya a yankin zai rage matsalolin sufuri da mazauna yankin ke fuskanta, musamman wajen samun damar zuwa asibiti da sauran wuraren kula da lafiya.
Ya ce, samar da hanyar kuma zai kara bunkasa harkokin kasuwanci, da karfafa dangantaka tsakanin al’umma da kuma saukaka wasu bukatu na yau da kullum da ke da matukar muhimmanci ga cigaban yankin.
Malam Ali Turbus ya kuma roki shugabannin karamar hukumar da sauran masu ruwa da tsaki da su tallafa wa al’ummomin wajen ganin an aiwatar da wannan aiki, yana mai cewa hakan zai inganta rayuwar jama’ar yankin.
A
Garuruwan da lamarin ya shafa sun hada da Kama, Takarda, Turbus, Mai Hassan, Kukayaskun Kaku, Fagen Kure, Jajeri da Kwanar Daniya
A cewarsa, hanyar da ake bukata za ta fara daga titin Hadejia-Gumel, ta ratsa cikin garuruwan da aka lissafa, sannan ta hade da hanyar Maigatari-Birniwa.
Usman Muhammad Zaria