Netanytahu Ya Fusta Da Furucin Kasar Canada Akan Kisan Kiyashi A Gaza
Published: 11th, April 2025 GMT
Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne.
Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya da karfi yana fada wa Fira ministan cewa, Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne.
Sai dai kuma kwana daya bayan abinda ya faru, fira ministan na kasar Canada ya lashe amansa inda ya bayyana cewa, bai ji kamlar kisan kiyashi ba, a cikin abinda aka ambata.
Wannan bai hana Fira ministan na HKI sukar takwaransa na Canada ba,tare da bayyana shi a matsayin mai kin jinin yuhudawa.
Su kuwa kungiyoyin kare hakkin bil’adama na cikin kasar Canada sun bayyana ja da bayan da Fira minstan ya yi da cewa, ba abinda za a laminta da shi ba ne, ya zama wajibi a gare shi da ya goyi bayan MDD da kungiyoyin kasa da kasa na kare hakkin bil’adama akan cewa; Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne.
Alaka a tsakanin HKI da kuma kasar Canada suna kara kamari,a lokacin da kungiyoyin kasa da kasa suke kara yi wa Tel Aviv matsin lamba akan kawo karshen yakin da take yi a Gaza.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kisan kiyashi Fira ministan kasar Canada
এছাড়াও পড়ুন:
MDD Ta Bukaci Taimako Dangane Rikicin Sudan Wanda Ya Isa Kasar Chadi
Shugaban hukumar yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi wanda ya ziyarce sansanonin yan gudun hijira na kasar Sudan a Chadi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen duniya su taimaka don kula da bukatun yan kasar sudan wadanda suke gudun hijira a kasar Chadi.
Grandi ya kara da cewa akwai bukatar agaji da gaggawa zuwa kasar Chadin da kuma sauran kasashen da suke daukar nauyin yan gudun hijira na sudan. A halin yanzu dai ana ganin mutane kimani 20,000 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu da dama suka ji rauni sannan wasu kuma suka zama yan gudun hijira.