Ministan Yaɗa Labarai Ya Zayyana Wa Masu Zuba Jari Na Faransa Irin Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Nijeriya
Published: 11th, April 2025 GMT
Idris ya gode wa kamfanonin Faransa da suka daɗe suna aiki a Nijeriya, irin su TotalEnergies, Lafarge, Peugeot, Danone, Alstom, Schneider Electric da sauran su, saboda gudunmawar da suke bayarwa a sassa daban-daban na ƙasar nan kamar makamashi, ababen more rayuwa, noma, lafiya da masana’antu.
Idris ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya tana kan “tafarkin sauyi da ba a taɓa ganin irin sa ba” wanda Ajandar Sabunta Fata ke ɗauke da shi.
Ya ce: “Waɗannan sauye-sauyen tarihi na gina tattalin arzikin da ya fi gasa, mai gaskiya da amfanar masu zuba jari, suna mayar da Nijeriya ƙofar shiga kasuwar masu saye ta Afirka wadda ke bunƙasa, ƙarƙashin Yankin Ciniki Cikin ’Yanci na Nahiyar Afirka (AfCFTA).”
Wasu daga cikin sauye-sauyen da ya yi nuni da su sun haɗa da:
Daidaita tsarin musayar kuɗi, cire tallafin mai domin daƙile asara, tsarin farashin wutar lantarki da ya dace domin ɗorewar sabis.
Sauran sun haɗa da sauye-sauyen haraji da ke inganta gaskiya da sauƙaƙe kasuwanci, sababbin dokoki da tsare-tsaren kuɗi da ke ba da goyon baya ga masu zaman kan su, sauƙaƙe harkokin shigo da kaya ta hanyar National Single Window, da sauye-sauyen dijital ciki har da tsare-tsaren shige da fice.
Ministan ya ce Nijeriya tana da fa’ida ta musamman ga masu zuba jari: ita ce mafi girman tattalin arziki a Afirka, yawan jama’a fiye da miliyan 220 — fiye da kashi 70 nasu kuma matasa ne ‘yan ƙasa da shekaru 35 — da kuma shekaru sama da 26 na dimokiraɗiyya ba tare da katsewa ba.
Ya ƙara da cewa gwamnati tana tabbatar da cewa tattalin arzikin ƙasar yana gudana ne ƙarƙashin ƙa’idojin doka, tare da tallafin hukumomin da suka haɗa da CBN, NIPC, SEC, da FCCPC.
Ministan ya ce a cikin watanni 20 kacal da gwamnatin Tinubu, an sauya tsarin kuɗi na ƙasa, inda aka samu ƙaruwa da kashi 3.84 na GDP a zangon farko na shekarar 2024, da samun ƙarin kuɗin shiga fiye da kashi 20, tare da rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen biyan bashi.
Ya ce: “Gwamnatin ta kasance mai ƙarfafawa wajen haɓaka sashen masu zaman kan su ta hanyar wasu muhimman shirye-shirye kamar Asusun Raya Ababen More Rayuwa na Sabunta Fata (RHIDF), Hukumar Bai wa Jama’a Lamunin Kaya ta Nijeriya (CrediCorp), Shirin Fadar Shugaban Ƙasa na CNG, Asusun Zuba Jari na Gidaje na MOFI (MREIF), da wasu da dama.
“Waɗannan shirye-shiryen suna shimfiɗa tubalin da za a iya dogaro da shi wajen jawo zuba jari na tiriliyan-triliyan na naira daga sashen masu zaman kan su a fannonin ababen more rayuwa, lamunin kayan masarufi, kiwon lafiya, gidaje, da sauran su.”
Ya kuma bayyana cewa bankunan Nijeriya suna ƙara faɗaɗa zuwa Turai, ciki har da buɗe ofisoshi a birnin Paris, yana mai cewa Nijeriya za ta ƙara samun wakilci a Faransa ta fannoni kamar ƙere-ƙere, fasaha da yaɗa labarai.
Ya gayyaci kamfanonin Faransa — musamman masu sha’awar harkar noma — da su ci gajiyar sababbin damarmakin da ke akwai a sashen kiwon dabbobi na Nijeriya, inda sabuwar Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi ta buɗe ƙofofin sababbin haɗin gwiwa.
Ya ce: “Dole ne mu shirya wa gaba da ƙwazo da fata mai kyau, tare da ƙarfin gwiwar da kakannin mu suka nuna.”
A yayin zaman sa a Paris, Minista Idris zai gana da manyan hukumomin yaɗa labarai da al’adu na Faransa, kamar France Médias Monde, ARCOM, Ma’aikatar Al’adu, da Thomson Broadcast, domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Faransa da Nijeriya a fannin watsa shirye-shirye da yaɗa labarai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji
Kamfanin Media Trust Limited na farin cikin sanar da al’umma cewa daga ranar Juma’a 11 ga watan Afrilun 2025, Rediyonta na Tusts Radio zai fara shirye-shiryen gwaji.
Tashar za ta fara yaɗa shirye-shiryenta a kan mita 92.7 a zangon FM a birnin tarayya Abuja da kewaye, kuma wannan na daga cikin tsare-tsaren da kamfanin ke bi na faɗaɗa aikin watsa labarai sama da shekaru 27 a Nijeriya.
An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarautaKamfanin Media Trust shi ne mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya a Nijeriya kuma mamallakin Trust TV da kuma Trust Radio a yanzu.
Ga waxanda ba su a birnin tarayya Abuja ko kuma suka yi tafiya za su iya kama tashar a shafinta na intanet a https://trustradio.com.ng ko a manhajar Radio Garden.
Haka kuma za a iya saurarenta shafukan Aminiya da Daily Trust da shafukan sada zumunta.
Da zarar tashar ta kammala gwajin za ta fara watsa ƙayatattun shirye-shirye da labarai tare da rahotanni masu ilimantarwa, faxakarwa tare da nishaɗantarwa.