Namibiya ta janye bizar shiga ga wasu manyan kasashe na duniya
Published: 11th, April 2025 GMT
Namibiya ta janye bayar da biza ga Amurka, Burtaniya, da wasu kasashe sama da 30.
Matakin, wanda majalisar ministocin Namibiya ta yanke tun a watan Yuli, ya fara aiki ne a ranar 1 ga Afrilu.
Ya zuwa yanzu, galibin kasashen Turai, ciki har da Jamus, babbar tushen yawon bude ido a Namibiya, sun ci gajiyar shigowa kasar ba tare da biza ba.
Sabuwar shugabar Namibiya da aka rantsar, Netumbo Nandi-Ndaitwah, tana ci gaba da shirye-shiryen soke bizar shiga kasar ga wasu Karin kasashe, ta yadda ‘yan kasashen za su iya shiga Namibia ba tare da biz aba.
Manufar hakan dai ita ce kafafa harkokin kasuwanci da yawon bude ido a kasar ga yan kasashen ketare, da kuma karfafa kawance da sauran kasashe.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato
Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato, sun nemo gawar wani makiyayi mai shekaru 16 da ya ɓace tare da ƙwato shanu sama da 50 da aka sace.
Daily Trust ta rawaito cewa, sojojin sun gano gawar makiyayin da ya ɓace tare da wasu Fulani makiyaya a ranar Juma’ar nan.
Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansaMakiyayin Abdullahi Muhammad mai shekara 16 da ya ɓace, kuma an samu rahoton an yi awon gaba da shanu sama da 70 a yankin Ariri, ƙaramar hukumar Bassa, a lokacin da suke kiwo a yankin.
Sai dai a baya, Danjuma Auta, babban sakataren ƙungiyar raya Irigwe (IDA), ya musanta batun satar shanu a yankin, yana mai zargin cewa an kashe mambobinsu da dama a cikin makonni uku da suka gabata, kuma suna fuskantar ƙalubale na hare-hare.
A cewar Ya’u Idris, shugaban Ƙungiyar MACBAN a garin Bassa, wanda ya tabbatar da samun nasarar gano gawar makiyayin da ya ɓace, sojojin OPSH tare da wasu makiyaya ne suka tsinto gawar a wani kabari mara zurfi, tare da wasu makiyaya a gaɓar kogi da ke kusa da babban yankin Ariri.
Ya ce, an fille kan makiyayin, aka datse hannunsa na hagu.
Da yake ƙarin bayani, shugaban ya ce, “Mun tono gawar kuma muka mayar da shi gida don yin sallar jana’iza, an ceto sama da kashi 80% na shanun, muna godiya ga jami’an tsaro musamman jami’an tsaron OPSH bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ƙwato gawar da shanu.”
Mai magana da yawun rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Samson Zhakom da DSP Alabo Alfred na rundunar ’yan sandan jihar, har yanzu ba su mayar da martani ga saƙon da wakilinmu ya aika masu kan wannan lamari ba.