Sanƙarau: An tabbatar da ɓullar cutar ga mutane 300 a Sokoto
Published: 11th, April 2025 GMT
Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da samun ɓullar cutar sanƙarau guda 300 a wasu ƙananan hukumomin jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Farouk Abubakar ne ya tabbatar da hakan a taron wayar da kan jama’a na kwana ɗaya da ƙungiyar raya unguwanni ta jiha (WDC) tare da haɗin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jiha da hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar suka shirya a ranar Juma’a.
Sai dai kwamishinan bai yi ƙarin bayani kan adadin mace-macen da aka samu tun watan Fabrairu da aka fara samun ɓullar cutar ba.
Ya ce har yanzu mutane 16 na ci gaba da karɓar magani a asibitoci yayin da sauran kuma aka sallame su.
A jawabansu daban daban, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kiwon lafiya a matakin farko na jiha, Dakta Muhammad Bello Marnona, da babbar sakatariyar hukumar, Dakta Larai Aliyu Tambuwal, sun yaba da irin hangen nesa na shugabancin hukumar ta WDC.
Sun ce, ana iya rigakafin cutar kuma sun shawarci mutane da su ziyarci cibiyoyin lafiya da ke kusa don samun magungunan da suka dace a duk lokacin da suka fuskanci wata matsala.
Shima da yake tsokaci shugaban yankin Malam Ya’u Muhammad Danda wanda mataimakinsa Alhaji Faruk Umar Garba ya wakilta ya bayyana taron a matsayin wanda ya dace.
A nasa jawabin, Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar wanda Hakimin Gagi, Alhaji Sani Umar Jabbi ya wakilta, ya yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu da jagororin gwamnatinsa na inganta lafiyar al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: sankarau
এছাড়াও পড়ুন:
Uwargidan Shugaban Kasa Ta Ba Matan Arewa Ta Gabas Su Dubu Tallafin Naira Miliyan 50
Sanata Oluremi Tinubu yt gana da sarakunan Taraba, ta kuma ba da gudummawar naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000, da kayan aiki dubu 10,000 ga ma’aikatan lafiya
Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta bukaci shugabannin gargajiya da su marawa shirin ta na sabon fata ta hanyar wayar da kan jama’a game da shirye-shiryen kiwon lafiya da ke gudana a fadin kasar.
Misis Tinubu ta yi wannan roko ne a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, yayin wata ganawa da sarakunan gargajiya a ranar Alhamis, wanda aka gudanar a dakin taro na uwargidan gwamnan jihar.
Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Bola Ahmed Tinubu da ta isa filin jirgin saman Danbaba Suntai a ranar Alhamis da tsakar rana, ta samu tarba daga gwamna Agbu Kefas da matarsa, Misis Agyin Kefas tare da manyan jami’an gwamnati, da kuma dimbin magoya bayan jam’iyyar PDP mai mulki a jihar da kuma babbar jam’iyyar adawa ta APC.
Mrs Tinubu ta kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Taraba, tare da rakiyar uwargidan mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Kashim Shettima, ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammed Ali Pate, da babban daraktan hukumar kula da lafiya matakin farko na kasa Dr Muyi Aina da dai sauransu.
Ziyarar ta na kuma da nufin karfafa gwiwar ma’aikatan kiwon lafiya na sahun gaba ta hanyar ba da tallafi da kuma sanin irin kokarin da suke yi, da kuma wayar da kan jama’a game da cutar kanjamau, musamman yaduwar cutar kanjamau daga uwa zuwa ’ya’ya.
Da take jawabi a yayin ganawarta da shugabannin gargajiya, Sen. Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa hada kai da sarakunan gargajiya zai taimaka wa gwamnatin tarayya wajen isar da sako game da samarwa da kuma maganin cutar kanjamau da tarin fuka kyauta, inda ta bayyana muhimmiyar rawar da suke takawa wajen hada kan jama’a.
Da yake mayar da jawabi, Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Taraba kuma Aku Uka na Wukari, HRM Manu Ishaku Adda Ali, ya bayyana ziyarar Misis Tinubu a matsayin alheri ga jihar.
Sai dai Sanata Oluremi Tinubu, jim kadan bayan ganawarta da shugabannin gargajiya, ta zarce zuwa filin wasa na Jolly Nyame, inda ta kaddamar da rabon kayayyakin sana’o’in ga ungozoma a fadin yankin Arewa maso Gabas.
A nata jawabin, ta kuma jaddada kudirin gwamnatin tarayya na samar da ayyukan kiwon lafiya da nufin rage mace-macen mata da kananan yara a fadin kasar nan.
A nasa jawabin, Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate, ya ce a yankin Arewa maso Gabas kadai, an horar da ma’aikatan kiwon lafiya 8,500, daga cikinsu 1,300 daga jihar Taraba.
A cewarsa, sama da cibiyoyin kiwon lafiya 1,000 ne ke samun tallafi a duk shekara daga asusun samar da kiwon lafiyai, ciki har da 170 a jihar.
Gwamna Agbu Kefas ya yabawa uwargidan shugaban kasar bisa wannan karimcin, inda ya ce jihar ta yi tarayya cikin hangen nesa na shirin sabunta fata.
A nata bangaren, uwargidan gwamnan, Misis Agyin Kefas, ita ma ta nuna jin dadin ta bisa yadda aka yi musu dauki, sannan ta yabawa ministan lafiya da walwalar jama’a bisa jajircewar sa.
A halin da ake ciki, Sanata Oluremi Tinubu ya mika kayan sana’o’in hannu guda 10,000 ga ungozoma a fadin jihohin Arewa maso Gabas shida, sannan ta mika chekin kudi naira miliyan 50 domin tallafa wa mata 1,000 a jihar Taraba.
Sani Sulaiman