An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa
Published: 11th, April 2025 GMT
’Yan bindigan da suka sace Fasto Samson Ndah Ali na cocin ECWA da ke Mararaba Aboro a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, sun sake shi sannan sun tsare wanda ya kai kuɗin fansar, Yusuf Shehu Ambi, wanda shi ne sakataren cocin.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, dattijon da ke matsayin jami’in koci na cocin ne ya kai kuɗin fansar, inda ’yan bindigar suka ƙi sakinsa bayan sun karɓi kuɗin.
“An saki faston, amma suka ci gaba da tsare mutumin da ya kai musu kuɗin. Ba mu san dalili ba, muna cikin fargaba da alhini,” in ji majiyar.
An sace Fasto Ali, mai shekara 30, daga gidansa da misalin ƙarfe 1 na dare a ranar 8 ga Afrilu, ƙasa da makonni biyu da naɗa shi zuwa cocin.
Tun da farko, masu garkuwar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan ɗari (N100m) ne daga shugabannin cocin.
Ƙoƙarin Aminiya na jin ta bakin hukumomin tsaro bai ci nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ECWA Karamar Hukumar Sanga
এছাড়াও পড়ুন:
Mai damfarar fursunoni ya gurfana a kotu a Kano
An gurfanar da wani mutum a gaban Kotun Majistare ta 17 a Kano bisa zargin shi da karɓar kuɗi a hannun wasu fursunoni da alƙawarin cewa zai fitar da su daga gidan yari.
Ana zargin wanda ake tuhumar, Kabiru Ahmed, da karɓar jimillar kuɗi naira dubu dari shida da goma daga Abdul Mukhtar, Bilkisu Shehu da kuma Muhammad Yahaya da sunan zai yi musu aiki a sako su daga gidan yari.
Lauyar masu gabatar da ƙara, Barista Sadiya Sabo, ta tuhumi mutumin da laifin damfara da kuma cin amanar da aka ba shi.
Wanda ake tuhuma ya amsa laifin, amma ya bayyana cewa ba shi kaɗai ya aikata wannan haramtaccen aiki ba.
’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan NajeriyaMai shari’a, Mai shari’a Hudu Haruna, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin ga ’yan sanda domin ci gaba da bincike, kuma ya ɗage shari’ar zuwa 20 ga watan Afrilu da muke ciki.