Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji
Published: 11th, April 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi wata muhimmiyar ganawar sirri da shugabannin sojojin Nijeriya a Abuja ranar Alhamis.
Taron wanda ya gudana daban-daban tare da babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Bala Abubakar na shirin sake tura wani sabon yunƙuri na ɗaukar matakin haɗa kai kan maharan Boko Haram.
Majiyoyi daga taron sun bayyana cewa, tattaunawar ta ta’allaka ne kan ƙarfafa ayyukan soji a yankin Arewa maso Gabas, da inganta musayar bayanan sirri da magance yawaitar hare-haren da ’yan tada ƙayar baya ke yi a baya-bayan nan.
Gwamna Zulum a ranar Talatar da ta gabata, yayin wani taron tsaro da aka gudanar a Maiduguri, ya koka kan yawaitar hare-haren da ’yan ta’addan ke kai wa a cibiyoyin farar hula da na sojoji, inda ya yi kira da a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki don kaucewa halin da ake ciki.
Zulum ya samu rakiyar Sanatoci masu wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, Borno ta Arewa Mohammed Tahir Monguno da Borno ta tsakiya Barista Kaka Shehu Lawan.
Sauran a tawagar gwamnan sun haɗa da: Mukhtar Betera Aliyu da Injiniya Bukar Talba, ‘yan majalisar wakilai da Farfesa Usman Tar, kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida na Jihar Borno.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babagana Umara Zulum Boko Haram
এছাড়াও পড়ুন:
Bam Ya Hallaka Mutane 8, Wasu da Dama Sun Jikkata A Borno
An ɗauki waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti a Maiduguri, inda ake ba su kulawar.
Har yanzu dai ba a tantance yawan waɗanda suka jikkata ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp