Har Yanzu Shugabanci NNPP Na Hannunmu – Tsagin Kwankwaso
Published: 11th, April 2025 GMT
Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta hana wadannan jami’an gudanarwa gudanar da taro, ko kuma jagorantar babban taron jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP.
Ko da yake, alkali mai shari’a Justice MA Hassan ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya bayyana cewa rikicin cikin gida na jam’iyyar kotun ba ta da hurumin sauyaran karar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Kwankwaso
এছাড়াও পড়ুন:
Gobara Ta Ƙone Shaguna 12 A Kasuwar Siminti Ta Oyo
A ƙalla shaguna 12 sun ƙone ƙurmus sakamakon gobarar da ta tashi da daddare a Agodi Gate, birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Lamarin ya faru ne a daren Alhamis a ginin Block A na kasuwar Siminti ta Mayegun, Araromi, kamar yadda hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta tabbatar.
Shugaban hukumar, Akinyemi Akinyinka, ya bayyana cewa jami’ansu sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:02 na dare, inda nan take suka tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Cfs Jimoh. Bayan isarsu, sun tarar da shaguna da dama na ci da wuta, amma cikin gaggawa suka dakile yaɗuwar gobarar zuwa sauran shagunan da ke kusa.
Gobara Ta Kashe Yaro A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Maiduguri Gobara Ta Ƙone Sabon Ginin Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Mata Na Jami’ar SokotoAkinyinka ya bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga wutar lantarki mai ƙarfi. Ya ƙara da cewa an kare dukiyoyi da darajarsu ta kai biliyoyin Naira a kasuwar, duk da cewa shaguna 12 sun ƙone baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp