Mahaifi ya yi wa ’yarsa ciki a Bauchi
Published: 12th, April 2025 GMT
’Yan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin ya ɗirka wa ’yar cikinsa mai shekara 17 ciki a yankin Kariya da ke Ƙaramar Hukumar Ganjiwa a Jihar Bauchi.
Kakakin ’yan sandan jihar, Ahmed Wakil ya ce an kama mutumin mai shekaru 50 ne bayan samun ƙara cewa ya yi wa ’yar tasa fyaɗe fiye da sau ɗaya a ɗakinsa.
Wakil ya ce a yayin bincike magidancin ya amsa cewa ya sha zakke wa ’yar tasa a gida, kuma bayan an yi mata gwaji a asibiti aka tabbatar cewa tana ɗauke da ciki wata uku.
Ya ce yarinyar ta shaida wa masu bincike cewa a lokacin da mahaifiyarta ta yi tafiya zuwa garin iyayenta a Ƙaramar Hukumar Ningi da ke jihar ne mahaifin nata ya yi amfani da damar ya riƙa lalata da ita.
An kashe mutum kan zargin satar kare a Bauchi Darasi daga rayuwar Dakta Idris AbdulAzeez Dutsen Tanshi ’Yan bindiga sun harbi alkali da ɗansa, sun sace mutane 13 a KatsinaBayan dawowar mahaifiyar ce ta lura da alamun juna biyu a tare da ’yar, kuma bayan ta titsiye ta, ta shaida mata cewa mahaifinta ne ya yi mata cikin.
Wakil ya ce rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, kuma kwamishinan ’yan sandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara.
Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana mai kara da cewa; Atsakanin watan Maris zuwa Aprilu na wannan shekara ta 20205 da ake ciki kadan, Isra’ila ta kai hare-hare har sau 224 akan gidajen mutane da kuma hemomin da ‘yan hijira suke ciki.
Har ila yau, hukumar ta kara da cewa; suna ci gaba gudanar da bincike akan wasu hare-hare 36 da sojojin Isra’ilan su ka kai da aka tabbatar da ya ci rayukan mutane da dama da su ka hada mata da kananan yara.
A nata gefen, kungiyar agaji ta “Red- Cross” ta yi gargadin cewa, kayan aikin da ake da su a cikin asibitocin da ake da su a cikin yankin sun kusa karewa.
Haka nan kuma kungiyar ta ce; ” A cikin yankuna da dama na Gaza, ba a iya samun ruwan sha, babu abinci, kuma babu wutar lantarki.
Ita kuwa ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza, ta yi kiran gaggawa domin a shigar da kayan aiki a cikin asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya. Haka nan kuma ta kara da cewa, da akwai masu fama da ciwon suga 80,000 sai masu hawan jini 110,000 ba su samun kula yadda ya dace.