HausaTv:
2025-04-12@21:43:50 GMT

MDD Ta Bukaci Taimako Dangane Rikicin Sudan Wanda Ya Isa Kasar Chadi

Published: 12th, April 2025 GMT

Shugaban hukumar yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi wanda ya ziyarce sansanonin yan gudun hijira na kasar Sudan a Chadi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen duniya su taimaka don kula da bukatun yan kasar sudan wadanda suke gudun hijira a kasar Chadi.

Grandi ya kara da cewa akwai bukatar agaji da gaggawa zuwa kasar Chadin da kuma sauran kasashen da suke daukar nauyin yan gudun hijira na sudan.

A halin yanzu dai ana ganin mutane kimani 20,000 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu da dama suka ji rauni sannan wasu kuma suka zama yan gudun hijira.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: yan gudun hijira

এছাড়াও পড়ুন:

Sudan ta kai karar Hadaddiyar Daular Larabawa a Kotun ICJ

Jakadan Sudan a Tehran, Abdul Aziz Hassan Saleh, ya tabbatar da cewa, za a gudanar da zaman farko na kotun kasa da kasa da ke birnin Hague a yau Alhamis, domin duba korafin da Sudan ta shigar kan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kan rawar da take takawa a yakin da ake ci gaba da yi a kasar, da kuma goyon bayan da take baiwa mayakan sa kai na Rapid Support Forces, tana mai kallonta a matsayin wani bangare na haddasa rikicin da ke faruwa a Sudan.

A wani taron manema labarai da ya gudanar a wannan Laraba 9 ga watan Afrilu a ofishin jakadancin Sudan da ke Tehran, jakadan Sudan ya yi tsokaci kan laifukan da dakarun RSF suka aikata a jihar Khartoum, inda ya jaddada faruwar munanan laifuka kan fararen hula, da suka hada da kama mutane ba bisa ka’ida ba, da take hakkin fursunoni, da amfani da yunwa a matsayin makami, da kuma cin zarafin mata.

Jakadan ya yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu sojojin Sudan sun kubutar da fursunoni kusan 4,700 da aka sace daga gidajensu, an tsare su ne cikin yanayi na rashin mutuntaka, inda gidajen yari ba su da ko da abubuwan more rayuwa.

Ya kara da cewa, “Rundunar RSF ba su bi ka’idojin shari’a ba wajen mu’amala da fursunoni, a maimakon haka, sun aikata munanan laifuka, har ma a kan kananan yara, ta hanyar yin garkuwa da su tilasta musu ficewa daga gidajensu har ma da karbar kudi daga hannunsu.

Ya kuma yi bayanin cewa har yanzu sojojin Sudan ba su samu damar shiga dukkan wuraren da dakarun RSF ke rike da fararen hula ba, inda ya ce an sace mata da ‘yan mata akalla 200 tare da kai su wuraren da ba a sani ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NDLEA Ta Kama Wani Mutum Mai Shekaru 75 Da Laifin Safarar Muggan Kwayoyi
  • Dalilin Nijeriya Na Karbo Bashin Dala Biliyan 12 Daga Kasar Japan
  • Iran: Akwai damammaki na diflomasiyya da za mu jarraba aniyar Amurka a kansu
  • Netanytahu Ya Fusta Da Furucin Kasar Canada Akan Kisan Kiyashi A Gaza
  • An Kafa Dokar Kai Da Komowa A Kudancin Kasar Syria
  • Sudan Ta Kai Karar HDL A Gaban Kotun Kasa Da Kasa Ta MDD
  • Shugaban Kasar Amurka Yace Yana Kokarin cimma yarjeniya da kasar China Dangane da Tiktok
  • Sojojin Sama Na HKI Kimani 1000 Guda New Suka Bukaci A Kawo Karshen Yaki A Gaza
  • Sudan ta kai karar Hadaddiyar Daular Larabawa a Kotun ICJ