Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassa Al-Mujtaba (a) 107
Published: 12th, April 2025 GMT
107-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.
///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).
A cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda siyasar khalifa na uku na rabon kudade inda muka bayyana yadda ya kebe wasu daga cikin danginsa na kusa da shi da kudade masu yawa, wannan kuwa duk tare da korafe-korafen wasu daga cikin manya-manyan sahabban manzon All..(s).
Mun ji yadda ya ware kudade masu yawa ya bawa, danginsa banu Umayya wadanda suka hada da Abusufyan, Marwan dan hakan, Da Hakam din, da Abdullahi dan Abisarkh da da sauransu. Wadanda wasunsu sun cutar da manzon All..(s) saida ya la’anesu wasu ya koresu daga madina, wasu daga cikinsu ya bada umurnin a kashesu ko da an gansu rike da rigar dakin Kaaba.
Sannan ya nisanta dangin manzon All…(s) a cikin mafi yawan al-amuransa, sannan kamar yadda zamu gani, ya nisantar da wadanda suke tare da su. Ya kuma wulakantasu da sauransu.
Wani abin mamaki da khalifa Uthman yayi shi ne, ya dauki gonar Fadak, wacce ya ga yadda Zahra (d) diyar manzon All..(s) ta kai ruwa rana da Khalifa Abubakar ya mayar mata don hakkinta ne, wanda manzon All..(s) ya bata, kyauta gareta ga kuma yayanta a bayanta, ya bawa Marwan dan Hakan.
Idan kuda tare da mu a cikin shirye-shiryemmu na baya, mun bayyana cewa ayoyin alkur’ani ne suka sauka suka mallakawa manzon All..(s) gonar fadak sannan wasu ayoyin suka sauka suka mallakawa Zahrah(s) wannan gonar Amma Khalifa Abubakar ya kwace ta daga Zahrah (a) sannan daga karshe bayan shekaru kimani 16 gonar da Fadak ta zama mallakar dan wanda manzon All…(s) ya kora daga Madina.
Kamar yadda muka bayyana wannan halin da Khalifa Uthman ya kaiga, sahabban manzon All..(s) da dama sun koka a gabansa, sun bayyana masa cewa bai yi dai-dai.
Al-amarin ya kaiga, Andurrahman dan Auf, wanda ya zabe shi a matsayin Khalifa, bayan wafatin Khalifa na biyu, ya fahinci cewa yayi barna, ya je yana fadawa Aliyu dan Abitalib (a) kan cewa, ka dauka takobinka, ni ma zan dauki takobina, don ya sauya daga alkawalin da yayi mani. Sai Imam Ali (a) ya yi banza da shi. Sannan ya kai ga a lokacinda Abdurrahman dan Auf zai mutu ya bar wasiyya kada a bar Khalifa Uthman yayi masa sallah.
A lokacinda yake bada wannan kyauta da danginsa, yana cewa su dangi nane, sai suka ce masa, shin Abubakar da Umar basa da dangi ne?, sai ya amsa da cewa, Abubakar da Umar sune neman lada wajen All..saboda hana danginsu dukiyar jama’a dake hannunsu, amma ni kuma ina neman ladar amma da basu dukiyar.
A lokacinda sukar ta yi yawa, sai Khalifa Uthman ya nemi afwar mutane, kan dukiyar jama’a da ya bawa danginsa.
Amma yayi haka ba tareda ya dawo da dukiyoyin da ya basu ba, kuma bai san cewa ba’a kyauta sai da dukiyar da ya mallaka ba?.
Amirulmuminina (a) ya bada kekkyawar misala a lokacinda mutane suka dora masa khalifanci a bayan kissan Khalifa Uthman.
Inda yayansa Akili dan Abitalib ya zo wajensa a kufa, cikin talaucinsa, ya bukaci Amirul muminina (a) ya bashi dukiya daga baitul malin musulmi kamar yadda Khalifa Usman yake yi don ya biya basussukan da ake binsa.
Sai nawa ne basussukan da ake binka? Sai yace . Dinari dub 100.
Sai Imam (a) yace, bani da su, amma ka jira idan an yi albashi in baka wani abu daga cikinsa.
Sai Akil yace masa, baitul Mali yana hannunka amma kana cewa sai ka rabon albashinka ya fita? Sai Imam yace masa, kana umurtata in baka dukiyar musulmi, bayan sun sanyani amintaccensu a kanta?. Har zuwa karshen maganarsu.
Kunji yadda shugaban kuma khalifan musulmi yakamata ya kasance.
Banda haka hadisai da dama sun tabbata daga manzon All..(s) wadan nan wadanda Khalifa Uthman yake rabawa dukiyar musulmi, la’ananu ne a cikin alkur’ani mai girma.
An karbo Hadisi daga Hakika ibnu Abihatin ya rawaito daga Ibn Amru daga manzon All..(s) yana cewa : Na yi mafarkin yayan Hakam dan Abi Ass sun haw kan mimbarori kamar birrai, sai All..ya sauka da iyar da take cewa {Kuma bamu sanya mafarkin da muka nuna maka ba face fitinah, ga mutane, da kuma la’ananniyar itaciya}…yana nufin Hakam da yakan da yayansa,
Ummulmuminina A’isha ta fadawa Marwan dan Hakam kan cewa na ji manzon All..(s). yana fadawa babanka, (Abil Ass dan Umayya) Ku ne itaciyar da aka la’anta a cikin alkur’ani, kuma hakika ya hana son wadanda suke adawa da shi, ya haramta sadar da zumunci da su. All..T yana cewa: {Ba zakat aba samun mutanen wadanda suka yi Imani da All..da ranar lahira suna son wanda suke kiyayya da All..da manzonsa (s).ko da kuwa sun kasance iyayensu, ko yayansu, ko yan uwansu ko kuma danginsu ba}. Akwai hadisai da dama da suka yi magana a kan wanna sanna.
Sannan dangane da walid dan uqba wanda khalifa na uku ya sa a matsayin walin Kufa, a baya mun bayyana yadda ya sami sabani da Abdullahi dan Masa’ud wanda ya kasance mai kula da baulmalin musulmi a Kufa, amma daga baya khalifa ya fadawa masa cewa shi mai ajiya ne amma bai da iko ya fadi inda za’a kashe kudaden.
A nan ne ya bar aikin ya kuma koma madina.
To wannan Walid din da nassan Al-kur’ani shi fasiki, inda All..Ta yake cewa : {..idan fasiki ya zo maku da labari ku nemi bayani ..}. Mazon All..ya aike shi zuwa karban Zakka a wajen Banu Mustalak, ya karbi zakka, amma sai ya je ya zagaya ya dawo yace aiki sun ki su bayar, sai manzon All..(s) ya shirya yaki zuwa can, kafin ya isa wannan ayar ta sauka ta kira shi fasiki.
Banda haka walid mutum ne mai cike da kiyayyan ga musulunci saboda mahaifinsa Ukbatu dan Abi rabii, ya cutar da manzon All…(s) a makama, inda ya tofa yau a faskansa ya zageshi, sannan manzon All..(s) ya ce masa idan na sameka a wajen makka sai na kashe ka.
Sai gashi ya je yakin Badar aka kama shi a cikin fursinonin yaki, manzon All..(s) ya fidda shi daga sauran fursinoni ya kuma sa Aliyu ya sare wuyarsa ya kashe shi. Don haka wadannan al-amura suka hadu suka sanya walid mikiyin manzon All..(s) da Aliyu (a) da ma addinin musulunci, to yaya Khalifa Uthman zai bashi shigabanci a kan musulmi, a kuma manya manyan birane kamar Kufa?
Garin kufa babban gari ne wanda ya tattara baki daga cikin sabbin musulunta da bayi wadanda suke bukatar sahabbai koprarro a cikin sanin hukunce hukuncen addini don ko koya masu addinin, su nuna masu halaye masu kyua na addini, wadanda basu musulunta daga cikinsu su jawosu zuwa ga addinin musulunci, da halaye masu kyau ko hikimomi na addini. Irin wadanan musulmi idan sun ga abinda Walid yayi ko yake yi, ina zasu yi sha’awar shiga addinin musulunci.?
Maganar walida bata karewa, don bayan ya sha giya sannan ya bada sallar asubaha yana cikin maye, sannan yayi masu sallar asubaha raka’o’ii 4 sannan ya juya y ace masu in kara maku ne? banda haka ya yi aman giya a mihrabin sallah. Sai mutanen kufa suka ga cewa ba zasu iya ba.
Suka cire zubensa na zinari suka je madina suka kai kararsa wajen Khalifa. Khalifa Uthman bai ji dadi ba, sai suka garzaya zuwa wajen Imam Aliyu dan Abitalib (a), wanda ya shiga wajen Khalifa ya yi masa magana, a nan ne ba da sonsa ba, ya aikawa walid ya dawo Madina, da ya dawo, wadan mutane suka zo suka shaida kan cewa ya sha giya. Sannan walida ya kasa musanta hakan. Sai hadda ya tabbata a kansa. Amma aka rasa wa zai zo ya yi masa bulala 80 wanda shi ne haddin All..ga wanda ya sha giya aka kasa, samu saboda an san irin kusancinsa da Khalifa.
A nan ne sai Aliyu dan Abitalib (a) ya zo ya dauki bulala ya zaneshi, ya zartar masa da hadda, Khalifa yana turmude da fuskansa, har yana tsawo ga Aliyu kada ka masa haka, kada ka masa haka..!.
Ana gama wannan sai Khalifa ya tausaya masa, ya bashi aikin karbo zakka daga kabilar Kalb, ya je ya karbo zakka, ya dawo Khalifa ya bashi dukkan abinda ya karbo, kamar yadda muka yi bayani a baya.
Sannan abin mamaki sai Khalifa ya tura Sa’id dan Ass wanda shi ma matashi ne daga cikin matasan banu umayya. Sannan halayensa mai yuwa kadan ne ya fi Walid. Shima ya je yayi tasa barnan a kufa.
Kada ku manta Imam Hassan (a) wanda muke kawo maku sirarsa yana sane da wadannan abubuwa, kuma yana rike da su. Saboda su zama masa darasi kan yadda zai tafiyar da al-amura a lokacinda khalifanci zai shiga hannunsa.
Ya san yadda zai fuskance wadannan mutane, wadanda suka zama fitina babba a cikin musulmi kawo ke tsammani.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All…ya kaimu wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Khalifa Uthman ya wadanda suka masu sauraro kamar yadda
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Rashin Ilimi Ke Cutar Da Rayuwar Al’umma
Ilimi Gishirin Rayuwa
Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko da wanda ake koya a wajen aiki ne ko wajen sana’a, ba lallai sai a cikin aji ba. Ana koyon ilimi na aiki da hannu, ko da baki ko a rubuce. Sannan yanzu da zamani ya canza, akwai kafofin sadarwa daban-daban da mutum zai iya samun ilimi ba tare da ya shiga aji ba. Akwai manhajoji irin su YouTube, LinkedIn, Facebook da sauransu da mutum zai iya shiga ya koyi abubuwa da dama na ilimi. Lallai yana da kyau iyaye su rika zaunar da yaran su suna koya musu karatu da ilimin rayuwa, tun daga matakin gida, ko a dauki nauyin mai koya musu, ko kuma a saka su a makaranta. Rashin sa yaro a makaranta na sa ya girma babu wayo, kuma zai rika rayuwar jahilci, da rashin sanin inda yake masa ciwo. Sannan gwamnati ta saukaka hanyoyin samun ilimi, a rika koyarwa da harshen uwa a matakin farko, a samar da ilimi kyau, a rika ba da tallafin karatu ga manya.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya hanyoyin da rashin ilimi ke cutar da al’umma suna da yawa domin shi ilimi jigo ne na rayuwar dan’adam muddun kuwa aka ce babu shi to dole abubuwa da dama ba za su tafi daidai ba, domin shi ilimi dan jagora ne ga duk kanin dan’adam shi ke haskawa mutum hanyar daya kamata ya bi da wacce ya kamata ya kaucewa don matsalolin da rashin ilimi ke haifarwa sun fi gaban kidayawa ko kirdado. To magana ta gaskiya a wannan fannin gwamnati ya kamata ta tashi tsaye wajen inganta fannin ilimin dama samar da shi kyauta ga duk kanin al’ummar kasa, sai kuma iyaye suma su tashi tsaye wajen kulawa da sa ‘ya’yansu a makaranta da kuma kula da zuwan yaran akan lokaci. To magana ta gaskiya kimiyya da fasaha tana bada gagarumar gudunmawa wajen saukaka samun ilimi a wannan zamani da muke ciki shi ya sa za ka ga dukkanin kasashen da suka cigaba ta fannin ilimin kimiyya da fasaha to sun fi samun cigaba a fannin ilimi. To amfanin ilimi ko muhimmancin ilimi ga rayuwar dan’adam ya fi gaban kidayawa ko kirdado domin sai da ilimi ne rayuwar take yin kyau kuma sai da ilimi ne ake samun cigaba a rayuwa. To hakika ya kamata irin wannan iyaye su sake tunani domin fa ilimi shi ne hasken rayuwa wanda duk ya rasa ilimi to ya rasa komai a rayuwarsa don haka ya kamata iyaye su tashi tsaye wajen kulawa da ilimin ‘ya’yansu.
Sunana Fatima Nura Kila A Jihar Jigawa:
Rashin ilimi na haifar da matsaloli musamman a cikin al’umma kamar su sata, fyade, rashin girmama manya duk wadannan rashin ilimi na kawo su. Hanyar daya kamata abi shi ne; Gwamnati ta zage damtse wajen tura yara makarantu da kuma saukaka karatu tun daga matakin firamare, har gaba da sakandare. Ilimin kimiyyya nada matukar amfani ga al’umma ta fuskar tabbatar da sauye-sauye tare da samar da cigaban rayuwa, musamman abin da ya shafi bunkasa tunanin dan’adam wannnan ba karamar taka muhimmiyar rawa yake ba. Ilimi jigo ne sannnan mahadin rayuwa ne, ilimi na da amfani musamman wajen zamantakewa da kuma kasuwancinmu na yau da kullum. Shawarar da zan basu shi ne su bar ‘ya’yansu su je makaranta domin Ilimi shi ne ginshikin rayuwa, mutum mai ilimi ma ya fita daban a cikin al’umma.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano Rano LGA:
Hanyoyin suna da yawa amma daya daga ciki ita ce; aikata ibada ba daidai ba da sabawa Allah kai tsaye. Samar da ilmi ta internet duk da mafiya yawan wasu mutanen tuni sun yi nisa ta wannan fannin. Wajen kirkirar wasu abubuwan da bamu saba ganinsu ba a yankunanmu. Daya daga cikin amfani Ilmi shi ne; aiki da shi a dukkan al’amuranka. Shawarata a garesu ita ce gaskiya su canja tunani kada iyaye su ga wai yanzu idan ka yi karatu ba a samun aikin yi a’a shi ilmi koda irin ‘yan iskan gari ne za ka ga sun bambanta da wadanda ba su yi ba, a saka yara su yi Ilmi ko wanne iri ne domin a can gaba za a ga amfaninsa. Allah ya sa mudace.
Sunana Aisha T Bello Jihar Kaduna:
Rashin ilimi cuta ce gaskiya, saboda ilimi shi ne kishin zaman duniya, yanzu misali; gida babu miji ya rasu in mata na da ilimi za ta nemi aiki dan ta kula da yaranta. Saboda yanzu duniya da zaran ba maigida ba masu kulawa da marayu Allah ne gatansu. Kimiya da fasaha na taka rawa sosai wajen kawo, cigaba ga al’umma bakidaya. Ga iyayen da basu tura yara makaranta gaskiya babbar cutarwa ce, domin kuwa yanzu duniya ta ci gaba, yanzu idan baka da ilimi kana ji kana gani ka zama dan kallo, don haka iyaye su daure su tura yara makaranta don cigaban al’umma bakidaya. Allah ya amfanar damu baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp