Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji
Published: 12th, April 2025 GMT
Jami’an tsaro Gwamnatin Tarayya suna sassauta wa masu kashe mutane babu gaira babu dalili a Jihar Filato, a cewar tsohon jihar na mulkin soji, Rear Admiral Samuel Bitrus Atukum.
Da yake tsokaci kan kisan gillar da ka yi wa mutane 52 tare da lalata kadarori na miliyoyin naira baya-bayan nan a yankin Ƙaramar Hukumar Bokkos, Atukum ya ce, “Ina da matsala kan yadda jami’an tsaro ke tunkarar matsalar.
“Daga kan tsaunuka mutanen nan suke saukowa ɗauke da makamai su halaka jama’a, sannan su ɓace, kuma a nan suke ɓoye makamansu. Saboda haka ya kamata jami’an tsaro su yi fiye da abin da suke yi yanzu.
“Kamata ya yi a ayyana waɗannan mutane a matsayin ’yan ta’adda, saboda ta’addanci suke yi, amma an kasa, sai a je ana kama masu ƙananan laifi da sunan manyan laifuka,” in ji Atukum wanda shi ne gwamnan Filato daga 1984 zuwa 1985.
Mahaifi ya yi wa ’yarsa ciki a Bauchi An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato Mutane 300 sun kamu da cutar sanƙarau SakkwatoYa bayyana cewa a lokacin da yake gwamna rikicin addini na ƙungiyar Maitatsine ya ɓarke, amma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci aka murƙushe shi, saboda gwamnati ta tari matsalar tun daga tushe kafin a je ko’ina.
Ya ce idan za a ɗauki irin matakin daga sama a kan matsalar tsaron Filato, shugaban ƙasa ya ba wa jami’an tsaro umarni a matsayinsa na Babban Kwamandan Tsaron Ƙasa, za su yi abin da ya kamata.
“Amma ba a ba da umarni ko ɗaukar mataki ba, sai mutane sun yi ta ƙorafi kan matakin da gwamnati ta ɗauka, sai a fito ana cewa za a kamo waɗanda suka aikata abin, a hukunta su daidai da abin da doka ta tanada. Wannan shi ne abin da muke ta ji.”
Ya ce, “Da ni ke da iko, da umarni da wa’adi ƙarara zan na wa jami’an tsaro cewa ga abin da nake so. Idan shugaban ƙasa da gaske yake kan matsalar tsaro, umarni kawai zai bayar kuma yana da tasiri a kan Majalisar Dokoki ta Ƙasa, duk abin da yake so za ta yi aiki a kai, kuma a tafi tare da ɗaukacin al’ummar ƙasa.
“Amma ya za a yi ka ce kana maganin abun, amma ba a ga alamar komai ba? Wa zai ɗauka da gaske kake, alhali ba a ga an kamo masu aikata laifin an hukunta su ba?
“A wannan yanayi da matsala ke fama da matsalar rashin aiki, mutane za su yi ta amfani da irin wannan giɓi wajen yin irin waɗannan aika-aika da muke gani.
“Har ta kai ga masu yin wannan ta’asa na ba da umarnin cewa ga wanda suke so a naɗa a matsayin shugaɓan wata hukumar tsaro, ko kuma a sauke wanda yake kai,” in ji tsohon gwamnan sojin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hukumomin tsaro Jami an Tsaro jami an tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Zamfara Ya Yi Jajen Rasuwar Dan Majalisa Aminu K/Daji
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu.
Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyar sa ga Majalisar Dokokin jihar da Iyalan mamacin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta aika da tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Mani Mummuni a yayin jana’izar ta marigayi Aminu K/Daji in Kauran Namoda.
“A madadin gwamnatin jiha,muna miƙa saƙon ta’aziyyar mu ga shugaban Majalisar Dokokin, sauran shugabanni a Majalisar, iyalai da al’ummar Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda ta Kudu.
“Muna kuma yin addu’a Allah ƙara ma iyalai jimirin jure wannan rashi. Muna kuma addu’ar Allah gafarta wa marigayin kurakuran sa.