Mutane Da Yawa Sun Jikkata Bayan Fashewar Bam A Wata Kasuwa A Ikeja
Published: 12th, April 2025 GMT
A ranar Juma’a da daddare, wata fashewar bama-bama a wata shahararriyar kasuwa a titin Kodesoh, Ikeja dake Lagos ta janyo raunuka ga mutane da dama. Shaidu sun bayyana cewa fashewar ta faru ne lokacin da wani mai kula da shagon kyamara ya yi kokarin bude wani kunshin da aka kawo.
Hukumar agajin gaggawa, tare da jami’an ‘yansanda daga tashar yankin G, EOD-CBRN Base 23 ta Ikeja, da ma’aikatan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihar Lagos (LASTMA), sun tura jami’ansu domin gudanar da ayyukan daukar matakai da tsaro a wurin.
Wani shaida gani da ido, Lucky Okoro, ya bayyana yadda ya samu damar gudu wa daga wurin fashewar, yana mai cewa, “kawai nayi ƙoƙarin shiga shagon, sai fashewar ta afku. Ban jima ba, sai na ga wutar tana kona wani mutum da wata mata a cikin shagon.” Wani shaidar, Olumide Gbeleyi, wanda yake daga wani otel kusa da wurin, ya bayyana cewa, “Mun ji hayaniyar fashewar kuma muka ga hayaki ya rufe ko’ina. Wata mata tana sayar da kayan ciye-ciye a waje ta ji rauni mai tsanani.”
Sule Aminu, wanda ya bayyana yadda abin da ya sani game da lamarin, ya zargi cewa kunshin mai ban mamaki yana dauke da wani abu da aka tura domin cutar da mai shagon.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sama da mutane 1,560 ne sukayi shahada tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki Gaza
Jami’an lafiya a Gaza, sun ce akalla mutane 1,563 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki a Zirin tun daga ranar 18 ga watan Maris, yayin da al’amuran jin kai ke kara ta’azzara a Gaza.
Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu a watan jiya ya zarce 1,560 a cewar jami’an kiwon lafiya.
A cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar yau Asabar, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 21 a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan.
An kashe mutane 50,933 tare da raunata 116,045 tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, in ji ma’aikatar a alkalumman data sabunta.
A cewar hukumar ‘yan gudun hijira ta Falasdinawa UNRWA, kimanin Falasdinawa 400,000 ne aka tilastawa barin muhallansu a fadin Gaza tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta fara aiki a watan Janairu ta ruguje kusan wata guda da ya gabata.