Yadda Amarya Za Ta Gyara Jikinta Har Zuwa Ranar Aure (II)
Published: 12th, April 2025 GMT
Ya zamto kowacce rana kina hada salad me yawa ki cinye shi, kar ki cika cin abin da zai birki ta miki ciki don kuwa shifa zai dinga rage miki ruwan jikinki ne, ki dage da cin kayan dadi sosai a wannan watannin.
(2b) Abubuwa masu mahimmacin da ya kamata su zama abincinki: Tuffa, Baure, Inibi, musanman sati 4 na karshe.
(3). Sinadaran gyaran jiki: To a nan fa matsalar take don gaskiya a wannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kin sha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda an fi son a ga amarya a cike ba za ki gane da gaske nake ba sai kin zauna nan a waje namiji ya gama tsara ki yana ce miki kin hadu kina jin kanki kawai sai ranar daran farko za ki fara ganin canji.
Saboda haka koda bayan sa ma akwai wasu supplement da za su kara miki kyau lokacin aurenki ya kamata ki nemo asalin original ki sha domin yawancin mata dakike ganin jikinsu sumul-sumul kamar su suka yi kansu ki gansu kamar a lashe yanzu duk su suke sha shi kuma gaskiya bai da wata matsala da yawa domin suna kokari wurin inganta shi sosai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Amarya Gyaran Jiki Kwalliya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi
Wasu mahara sun harbe wasu mata biyu har lahira tare da banka musu wuta a gonakinsu da ke ƙauyen Okete a Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi.
Lamarin ya faru ne a lokacin da kowacce daga cikin matan biyu ke tsaka da kula gonarta.
An ce maharan sun yi musu ruwan harsasai baya wata taƙaddama da ta ɓarke, sannan suka tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Wani mazaunin yankin ya ce, “Muna cikin juyayi tun da muka samu labarin harin da aka kai wa ’ya’yanmu mata a gona. Sun je gonakinsu ne domin su kula da su a ranar Laraba, abin takaici sai wata ta ƙaddamanta ɓarke, kuma maharan, waɗanda ake zargin makiyaya ne, suka harbe su har lahira.
“Mun yi tunanin za mu ɗauko su da rai ne lokacin da muka samu labarin a ranar Laraba, amma sai muka iske gawarwakinsu an yi musu ruwan harsasai da kuma ƙuna a jikinsu.”
Cutar Kwastomomi: NERC ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar N628m ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja