Iran da Amurka zasu ci gaba da tattaunawa a mako mai zuwa
Published: 12th, April 2025 GMT
An kammala zagayen farko na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a babban birnin Muscat a shiga tsakanin kasar Oman.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da Steve Witkoff, manzon musamman na shugaban Amurka kan harkokin yankin gabas ta tsakiya ne suka jagoranci shawarwarin yau Asabar.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce bangarorin sun yi musayar ra’ayi game da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, da kuma dage takunkumi.
Ya kara da cewa an gudanar da shawarwarin ne cikin yanayi mai ma’ana kuma bisa mutunta juna.
A karshen sama da sa’o’i biyu da rabi na tattaunawar, shugabannin tawagogin Iran da na Amurka sun yi jawabi na ‘yan mintoci kadan a yayin da suke barin wurin taron a gaban ministan harkokin wajen Omani,” in ji ma’aikatar.
Bangarorin kuma zasu sake tattaunawa nan da mako mai zuwa, saidai ba’a bayyana takaimaimai wajen da tattauanwar za ta wakana ba.
A gefen tattaunawar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baghaei ya shaidawa kafar yada labarai ta IRIB a birnin Muscat cewa, Iran na da manufa guda daya tabbatar da muradun kasa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Iran: Akwai damammaki na diflomasiyya da za mu jarraba aniyar Amurka a kansu
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, ma’a, kwana guda gabanin tattaunawar da ake jira a kasar Oman tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar kasar Iran, damammaki da daman a diflomasiyya da Amurka za ta iya tabbatar da aniyarta a kansu
Baqaei ya rubuta a dandalin X, “Ya kamata Amurka ta mutunta wannan shawarar da aka yanke duk da cewa ana fama da rikici.”
“Ba za mu yanke hukunci ba, Muna da niyyar tantance niyyar dayan bangaren kuma za mu tabbatar da hakan a wannan Asabar,” in ji jami’in diflomasiyyar na Iran, ya kara da cewa Iran “za ta yi tunani kuma ta mayar da martani ga kowane mtaki.”
A ranar Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya ba da sanarwar cewa gwamnatinsa za ta shiga tattaunawa da Iran.
A ci gaba da tattaunawar da za a yi a ranar Asabar, bangarorin biyu sun yi musayar kalamai masu zafi, inda Trump ya yi barazanar daukar matakin soji idan tattaunawar ta ci tura.
Dangane da gargadin na Trump, wani babban mataimaki ga jagoran Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya ce Iran za ta iya daukar matakan da duk ta ga sun dace a kan wannan lamari.
Taron na ranar Asabar na zuwa biyo bayan wata wasika da Trump ya aikewa Sayyed Khamenei a watan da ya gabata, inda ya bukaci Tehran da ta shiga tattaunawa tare da yin gargadin cewa matakin soji na kan teburi idan Iran ta ki amincewa.
Tehran ta bayyana aniyar ta na shiga tattaunawar kai tsaye amma muddin Washington ta ci gaba da manufofinta na “mafi girman matsin lamba”.