Yaya ‘Yan Siyasar Amurka Ke Kasafta Harajin Ramuwar Gayya?
Published: 12th, April 2025 GMT
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Trump ya janye harajin da ya kara wa duniya, amma ya laftawa China 125%
Shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da haraje-harajen da ya lafta kan kayayyakin da ke shiga kasar daga kasashen duniya, sai dai ya kara harajin da kashi 125 ga kasar China.
A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce za a rage haraje-harajen zuwa kashi 10%, sai dai za a kara wanda aka lafta kan kayan China zuwa kashi 125%.
Donald Trump ya kuma zargi China da nuna rashin girmamawa da kuma zaluntar Amurka.
Kafin haka, China ta sanar da kara haraji kan kayan Amurka da ake shiga da su kasarta zuwa kashi 84% – inda Chinar ta zargi Amurka da barazana kan kasashen duniya.
Matakin na zuwa ne jim kadan bayan da Beijing ta mayar da martani ga karin harajin da Washington ta yi a baya
Trump ya kuma yi nuni da cewa, ba kamar China ba, “wadannan kasashen, bisa ga kwakkwarar shawarata, ba su mayar da martani ta kowace hanya, ko siffa, a kan Amurka ba.”
Kazalika, jami’an Amurka sun bayyana a wannan rana cewa, yanzu kasashe ko kungiyoyin kasa da kasa fiye da 50 sun riga sun tuntubi Amurka kan matakin nata na harajin kwastam.
Wannan lamarin ya shafi kasashe 70 na duniya, wani abu da ya haddasa barkewar rikicin kasuwanci tsakanin Amurkar da kasashe da dama, musamman manyan kasashen da take huldar kasuwanci da su, kamar China da kuma kasashen Tarayyar Turai.
Su ma kasashen Tarayyar Turai sun lafta harajin kashi 25 cikin dari kan kayan da Amurka da ake shiga da su yankin.