Aminiya:
2025-04-14@19:07:04 GMT

Mutum ɗaya ya mutu a faɗan ƙungiyar asiri a Maiduguri

Published: 13th, April 2025 GMT

Wani matashi ɗan shekara 18 mai suna Bakura Muhammed, ya gamu da ajalinsa a wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin matasa masu gaba da juna da ake wa laƙabi da Malians a Maiduguri.

Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zaga-zola Makama cewa, rikicin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar 4 ga watan Afrilun nan a yankin Ajari da Tashar Lara, inda matasan ɓangarorin biyu suka yi artabu da juna.

An daɓa wa wanda aka kashen wuƙa a ciki, wanda ba tare da ɓata lokaci ba jami’an tsaro na Maidugurin suka ɗauke shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa.

Wata majiyar ‘yan sanda ta ce, an kama wasu mutane bakwai masu shekaru tsakanin 15 zuwa 24.

Majiyar ta bayyana sunayen ababen zargin da aka kama da suka haɗa da Ba’abba Kyari mai kimanin shekara 20 sai Ali Alhaji Goni Ali dan shekara 20 da Muhammed Audu mai kimanin shekara 18, sai Ali Isa mai shekara 15 da Adam Sabir mai shekara 15 da Mohammed Tujja shekaru 17 da Usman Kasim dan shekara 24

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: jihar Borno Ƙungiyar Asiri

এছাড়াও পড়ুন:

An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo

Jami’an tsaron Jihar Edo sun sake kama wasu mafarauta hudu daga Kano, makonni kadan bayan kisan gilla da ’yan bangar Jihar Edo suka yi wa ayarin wasu mafarauta 16 daga jihar Kano a jihar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, ta ce mafarautan da aka kama sun fito ne daga Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano, kuma suna dauke da bindigogin toka guda uku, da adduna da wukake a lokacin da aka kama su.

Kakakin ’yan sanda an jihar, CSP Moses Yamu, ya ce kanawan da aka kama mafarauta ne ba kamar yadda ake yadawa a kafofin sada zumunta cewa makiyaya ba ne.

Ya bayyana cewa jami’an kungiyar tsaro ta Jhar Edo ne suka kama mafarautan sannan suka damka su ga ’yan sanda inda ake yi musu tambayoyi a ofishin ’yan sanda da ke yankin Ikpoba Hill.

’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken Tinubu

Ya ce an, “An kama mafarautan da suka fito daga Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa yankin Uvbe da ke Karamar Hukumar Orhionwon a Jihar Edo. A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike.”

Da haka Kwamishinan ’yan sandan jihar, Monday Agbonika, ya gargadi jama’ar jihar da su guji yada abin da ba gaskiya ba ne game da lamarin, domin yana iya tayar da zaune tsaye.

Idan ba a manta ba, a cikin watan Ramadan, gab Sallah Karama ne ’yan banga suka yi wa wasu mafarauta 16 daga Jihar Kano da ke hanyarsu ta komawa gida hutun sallah kisan gilla a yankin Uromi da ke jihar, lamarin da ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya, inda har yanzu ake kokarin shawo kansa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo
  • Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum Ɗaya A Bauchi, Wasu Sun Jikkata
  • Inganta Rayuwar Al’umma: Amurka Da Ƙungiyar Kasuwanci Ta Nijeriya Sun Karrama Gwamna Lawal
  •  Nigeria: Wani Bom Da Ya Tashi A Maiduguri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 7
  • Fashewar bam a mota ta kashe mutum takwas a Borno
  • An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato
  • An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano
  • Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji
  • NDLEA Ta Kama Wani Mutum Mai Shekaru 75 Da Laifin Safarar Muggan Kwayoyi