HausaTv:
2025-04-14@20:26:06 GMT

HKI Ta Jefa Boma-Bomai A Kan Asbiti Tilo Da Ya Rage Yake Aiki A Arewacin Gaza

Published: 13th, April 2025 GMT

Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin.

Har’ila yau hare-haren sun lalata bangaren Iskar Oxigen na kula da wadanda suke bukatar kula mai tsanani a asbiti. Kuma sanadiyyar haka mutane da dama sun rasa rayukansu awannan bangaren daga ciki har da wani yaro dan shekara 12 wanda ya ji rauni a kai.

Razan Al-Nahhas wani likita mai aiki a bangaren  kula na gaggawa a asbitin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa wannan asbitin ne kawai dama yake aiki a arewacin Gaza, kuma a halin yanzu babu wani asbitin da ya rage a yankin.

Labarin ya kara da cewa bayan  wadannan hare-hare kan asbitin na Al-Ahli, mutane da dama basu san inda zasu je don samun jinya ba.

Likitan ta kara da cewa kafin hare-hare na safiyar yau Lahadi dai marasa lafiya wadanda aka yankewa kafafu da kuma wadanda suka ji rauni a kai da kuma kirjinsu ne suka fi yawa a cikinsa. Sannan a halin yanzu babu inda zasu je sai wasu kananan asbitoci wadanda basu da kayakin aiki na kula da su. Kuma tuni wasu sun mutu bayan harin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis

Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya.

A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya tare da samar da “yankin tsaro” a can.

Sanarwar da ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Katz ya fitar ta ce sojojin sun karbe ikon “Morag axis, wanda ke ratsa Gaza tsakanin Rafah da Khan Yunis.”

Katz ya kuma yi kira ga Falasdinawa da su fara kaura zuwa yamma, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kara kaimi da fadada ayyukan soji zuwa wasu yankuna a cikin mafi yawancin Gaza.

IDF ta ce ta karɓe da abin da ta bayyana da cibiyar tsaronta da ta yi wa laƙabi da ”Lungun Morag”, sunan wani ginin da Isra’ila ta taɓa yi tsakanin biranen biyu.

A yanzu haka sojojin Isra’ila na gina titi a wurin, da nufin samar da wani wuri da Isra’ila ke iko da shi da ya raba Zirin Gaza.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Hamas ke cewa ta aika wakilanta zuwa Masar domin tattaunawa da masu shiga tsakani kan yiwuwar dawo da yarjejeniyar zaman lafiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas ta ce a shirye take ta sako dukkan fursunonin Isra’ila da suka rage, domin musanya fursunoni”
  • Gaza: Mutane 38 Sun Yi Shahada A Yau Litinin
  • Bam Ya Halaka Mutum 8, Ya Jikkata Wasu Da Dama A Borno
  • Jiragen Yakin Kasar Amurka Suna Rusa Cibiyoyin Ilmi A Hare-Haren Da Suke Kaiwa Kasar Yemen
  • Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis
  • Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?
  •  Limamin Tehran: Iran Ba Ta Tsoron Tattaunawa
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • Yemen Ta Maida Martani Kan Wasu Cibiyoyin Ajiyar Makamai A Yaffa Don Tallafawa Gaza