Inganta Rayuwar Al’umma: Amurka Da Ƙungiyar Kasuwanci Ta Nijeriya Sun Karrama Gwamna Lawal
Published: 13th, April 2025 GMT
Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta karrama gwamna Lawal tare da gwamnonin Akwa Ibom, Kaduna, da kuma jihar Legas.
“A jiya a Legas, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da ƙaddamar da Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban ƙungiyar na 20.
“Taron mai taken ‘Ƙarfin Haɗin Kai: Shekaru 65 na inganta dangantakar tattalin arzikin Nijeriya da Amurka’ ya samu halartar manyan jami’an Amurka da Nijeriya da kuma ‘yan kasuwa.
“Ƙungiyar ta amince da goyon bayan da Gwamna Lawal yake baiwa harkokin kasuwanci a jihar Zamfara, musamman a fannin noma.
“Karramawar da aka baiwa gwamnan na nuni ne da irin kwazonsa na jagoranci, da kwazonsa na inganta ilimi, da kuma jajircewarsa wajen magance matsalar rashin tsaro.
“Ƙungiyar ta kuma yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa inganta rayuwar al’ummar Zamfara ta hanyar ba da fifiko wajen samar da kiwon lafiya, ilimi, noma, da kuma ayyukan ƙarfafawa guiwar al’umma.”
Yayin karbar lambar yabon, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirinsa na inganta rayuwar al’ummar Jihar Zamfara ta hanyar inganta ayyukan yi.
“Ina so in gode wa shugabannin ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka da suka ga na cancanci wannan karramawa, hakan zai ƙara min kwarin guiwa na ƙara himma, wannan na ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara ne.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya da
এছাড়াও পড়ুন:
Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?
Lamarin ya faru ne a lokacin da matashin mawakin yake kan dandamali ya na rera daya daya daga cikin fitattun wakokinsa, har zuwa lokacin wannan rahoto, Bilal Billa bai fitar da wata sanarwa a kafafen sadarwar ba, amma kuma faruwar lamarin ya janyo cece kuce inda wasu a bangare guda ke ganin abin da aka yi wa mawakan ya yi daidai yayin da wasu kuma ke ganin hakan bai dace ba.
Wasu na ganin cewar kalmar nan ta bahaushe da ya ce “Bokan Gida Bai Ci”, shi ne ke faruwa a kan wadannan mawakan, wasu kuma na ganin wannan wata hanya ce da aka dauko domin dakile tauraruwarsu da ke haskawa, wasu kuma ke cewa wannan kawai wata hanyar nuna hassada ce da mutanen arewacin Nijeriya ke amfani da ita saboda a kudancin kasar irin wannan ba kasafai yake faruwa tsakanin mawaka da sauran al’umma ba.
Ko ma dai minene dalilin da ya janyo jifar mawakan, ba zai rasa nasaba da banbancin ra’ayi ba kokuma rashin jituwa a tsakanin mawaka da masu saurarensu akan wani abinda su ka taba fafi ko aikatawa a cikin wakokinsu, sau da dama mawakan siyasa na fuskantar wannan kiyayya daga masoyansu wadanda ra’ayinsu ya saba a siyasance.
A wani lokaci can baya shahararren mawakin siyasa a Nijeriya Alhaji Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara ya fuskanci kalubale daga mutane da suke da banbancin ra’ayin siyasa, har ta kai ga wasu fusatattun matasa sun farmaki ofishinsa domin nuna fushi a kan wakokin suka ko tsangwama da yake yi wa gwaninsu a siyasance.
Amma kuma ba kasafai ake samun mawakan nanaye, nishadi ko soyayya da samun tsama tsakaninsu da masoyansu ba, duba da cewar mafi yawan lokutan mawakan kan sosa masu inda yake yi masu kaikayi a fagen soyayya, amma kuma wadannan al’amura da su ka faru a wannan shekarar ya jefa tambaya a zukatan wasu da dama a kan MI YA JANYO JIFAR MAWAKA A AREWACIN NIJERIYA.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp