Aminiya:
2025-04-15@04:34:07 GMT

’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara

Published: 13th, April 2025 GMT

’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje fiya da 10 a yankin Biyabiki da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

’Yan ta’addan sun cinna kona wuraren ne bayan sallar Isha’i a ranar Asabar a wani da ake zargin na ramuwar gayya ne kan kashe Isuhu Yellow, kanin wani jagoran ’yan bindiga mai suna Adamu Aliero.

Shaida sun ce da  misalin karfe 8 na dare ne ’yan bindigar da ake zargin yaran kasurgumin dan bindiga Adamu Aliero ne suka kai harin a kan babura, inda suka banka wa wuraren wuraren wuta, sannan suka tsere ba tare da taba mazauna ba.

“Wuraren da suka cinna wa wuta sun hada da masallacin Juma’a da wani karamin asibiti da kuma gidaje kimanin 10 da suka lalata,” in ji wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa.

A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a Majalisa

Ana kyatuta zaton harin na da alaka da kashe Adamu Yelow a wani harin kwanton bauna da shi da tawagarsa suka kai wa jami’an tsaro, a yankin Keta, kimanin makonni uku da suka gabata, amma jami’an tsaron suka aika su lahira.

Tun da farko a ranar sai da ’yan ta’addan sun kuma kai wani hari a kauyen Tsageru a ranar, inda suka kona gidaje da dama.

Wani mazaunin yankin ya ce, “Ba mu san wace butaka suke neman cim ma da kona gidaje da kayan gwamnati da suke yi ba; Tun da aka kashe Isuhu Yellow yankunanmu ke ta fuskantar barazana, don haka muna kyatata zaton wanna harin ramuwar gayya ce.”

Wakilinmu ya yi kokarin tattaunawa da kakakin ’yan sanda na Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, domin samun karin bayani, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba, bayan ya yi ta kiran wayar jami’in.

Wannan hari na kara nuna alamr ci gaban matsalar tsao a Jihar Zamfara inda ’yan bindiga ke kara cin karensu a yankunan karkara, duk kuwa da kokarin hukumomin tsaro na yi wa tufkar hanci a yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan ta adda hari Zamfara yan bindiga Yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jihar Filato

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan harin da aka kai  Jihar Filato wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40.

A cikin wata sanarwa, Shugaban kasa ya la’anci wannan tashin hankali tare da mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang, Gwamnatin Jihar, da al’ummar Filato.

Sanarwar da Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan Harkokin Yada Labarai Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, ta bukaci Gwamnan da ya nuna cikakken ikonsa wajen warware rikicin da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin soyayya da hadin kai a maimakon  bambancin addini da kabila.

Ya bukaci shugabannin al’umma, da na addinai, da ma na siyasa a ciki da wajen jihar, da su hada kai domin kawo karshen ramuwar gayya da rikice-rikicen da suka jima suna addabar al’umma.

“Ya zaman wajibi a kawo karshen rikicin da ke faruwa tsakanin al’umma a Jihar Filato wanda ya samo asali daga rashin fahimta tsakanin kabilu da addinai daban-daban.” In ji Shugaba Tinubu.

“Na umarci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan wannan rikici, da gano wadanda ke da hannu a shirya wadannan ayyukan tashin hankali. Ba za mu amince da wannan barna da hare-haren ramuwar gayya ba. Ya isa haka.

Ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ba Gwamna Mutfwang da Gwamnatin Jihar Filato goyon baya wajen karfafa tattaunawa, inganta zaman tare, da tabbatar da adalci don magance wannan rikici har abada.

 

Daga Bello Wakili

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun kama ’yan bindiga 12 a Nijar
  • Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jihar Filato
  • ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato
  • Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
  • An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo
  • Fashewar bam a mota ta kashe mutum takwas a Borno
  • An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato
  • An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina
  • Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas