An kama miyagun kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
Published: 13th, April 2025 GMT
Jami’an tsaro sun kwace miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 300 sannan ta kama mutane 650 da ake zargi a Jihar Kano.
Kwamitin Dawo da Zaman Lafiya da Kyautata Dabi’un Matasa ta Jihar Kano ce ta yi wanna kame a fadin jihar, kamar yadad ta bayyana a rahotonta.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya bayyana, ya bayana cewa mutum 150 daga ckin adadin an kama su ne kan laifukan dabanci da kwacen wayada da dangoginsu.
Kwamitin ya ce aikin haɗin gwiwar, ya yi wannan nasara ne bayan da suka kai samame a kan maboyar masu aikata laifuka da aka gano a kananan hukumomi takwas da ke garin Kano.
An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo ’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken TinubuHukumar ta bayyana cewa an gudanar da aikin ne tare da ’yan sanda da Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) da Hukumar Kula da Gidajen Yari da Hukumar Shige da Fice, da sauran hukumomi.
Da yake jawabi a wani taro da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, Shugaban Rundunar, Dakta Yusuf Ibrahim, ya ce ƙwace miyagun ƙwayoyin da aka kiyasta kimarsu a Naira miliyan 300 zai taka muhimmiyar rawa.
Ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da tallafin al’umma ke takawa wajen dorewar ƙoƙarin Rundunar na inganta tsaron jama’a.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam, ya yaba wa nasarorin da Rundunar ta samu, yana mai tabbatar da kudurin gwamnatin jihar na magance ƙalubalen tsaro ta hanyar irin waɗannan matakai masu ƙarfi. Sa’annan ya jaddada buƙatar haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da al’umma don samun ɗorewar tsaro.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, ya yaba da ingancin ayyukan da aka gudanar bisa ga bayanan sirri, yana amai kira da a kafa wata kotu ta musamman domin hanzarta shari’ar waɗannan laifuka.
Kwamandan Hukumar NDLEA na Jihar, Abubakar Idris, ya yaba da haɗin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaro kuma ya yi kira da a ci gaba da shidon magance matsalolin tsaro a Jihar Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kwayoyi
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano
’Yan sanda sun cafke wasu mutum takwas da ake zargi da faɗan daba a yankin Ƙofar Na’isa zuwa Ƙofar Ɗan Agundi da ke ƙwaryar birnin Kano.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a LegasKiyawa ya ce a ranar Alhamis da ta gabata ce suka samu kiraye-kirayen waya cewa wasu sun fito da makamai suna faɗan daba, lamarin da ya sanya aka tura jami’ai domin ɗaukar mataki.
Kakakin ’yan sandan ya ce a wannan lokaci babu wanda aka kama sakamakon arcewa da masu faɗan daban suka yi.
“Wasu sun fito faɗan daba, sun ji wa kansu raunuka a Ƙofar Na’isa, amma ba wanda ya zo wajen ’yan sanda a kai shi asibiti,” a cewar Kiyawa.
Sai dai Kiyawa ya ƙara da cewa jami’ansu sun sake komawa unguwar da daddare, inda suka cafke mutum takwas da raunuka a jikinsu da wuƙaƙe.
Kazalika, ya ce sun tattara sunayen mutane daban-daban da ake zarginsu da faɗace-faɗacen daba kuma nan ba da jimawa ba za su shiga hannu.
Aminiya ta rawaito yadda ake zaman ɗar-ɗar a yankin Ƙofar Na’isa da kuma Ƙofar Ɗan Agundi tun bayan dawowar faɗan daban a yayin bukukuwan sallah ƙarama da aka yi kwanan nan.