Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
Published: 14th, April 2025 GMT
A ranar Lahadi Liverpool ta sake matsa ƙaimi a gasar Firimiya bayan ta doke abokiyar karawarta West Ham United ci 2-1 a filin wasa na Anfield dake birnin Liverpool, yayin da Mohamed Salah ya kafa tarihin cin ƙwallaye a kakar wasa ta bana, sakamakon ya sa Liverpool ta samu tazarar maki 13 tsakaninta da Arsenal dake matsayi na biyu a kan teburin gasar.
Yayinda yake saura wasanni shida a kammala gasar, Liverpool na buƙatar maki 3 kacal domin lashe gasar a karo na biyu tun bayan da aka sauya wa gasar suna da fasali, West Ham na matsayi na 17 da maki 35 akan teburin gasar.
Ba Zan Ci Gaba Da Zama A Liverpool Ba -Salah Salah Ya Ƙulla Sabuwar Yarjejeniyar Shekaru 2 Da LiverpoolESPN ta ruwaito cewa kafin fara wasan, an yi shiru na minti daya a Anfield don nuna girmamawa ga mutane 97 da iftila’i ya rutsa da su a filin wasa na Hillsborough a shekarar 1989, sai dai magoya bayan Liverpool sun ɓarke da ihu jim kaɗan bayan shirun, inda suke nuna jin daɗinsa dangane da sabon kwantiragin shekaru biyu da Salah ya sanya hannu a tsakiyar mako.
A wannan wasan ne Salah ya kafa tarihin wanda ya fi zama komai da ruwanka a wajen zura ƙwallaye a raga a wasannin gasar inda ya zura ƙwallaye 27 ya kuma taimaka aka jefa 18, ana alaƙanta Salah da komawa ƙasashen Larabawa domin cigaba da taka leda, amma kuma sabon kwantiragin da Salah ya sakawa hannu ya sa zai cigaba da zama a Anfield tsawon shekaru biyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kebbi Za Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai A Saudiyya
Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen daukar nauyin dalibai 70 zuwa Masarautar Saudiyya domin karatun digiri a fannoni na addini da na zamani.
Wannan na daga cikin shirin “Kaura Capacity Building Project 2025“ karkashin ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jihar.
A yayin wani taron manema labarai, mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin addinali, Injiniya Imran bn Usman, ya bayyana cewa kowanne daga cikin kananan hukumomi 20 na jihar za su ba da sunayen dalibai uku, yayin da aka ware wa babban birnin jihar, Birnin Kebbi, guraben dalibai 10.
Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ce za ta dauki nauyin tafiyar daliban zuwa Saudiyya, yayin da gwamnatin Saudiyya za ta dauki nauyin karatunsu da walwalarsu bayan isarsu.
Mai ba da shawarar ya kara da cewa, ana sa ran kowacce karamar hukuma za ta gabatar da dalibai maza biyu da mace daya, don neman guraben karatun digiri a fannin addinin Musulunci ko sauran fannoni na zamani.
Ya kuma kara da cewa, an kammala shirin tura limaman masallatai Jumu’a zuwa kasashen waje domin horo na gajeren lokaci a fannin yadda ake gabatar da huduba da Hadisi, don kara inganta tasirinsu yayin gabatarda Sallah.
Daga Abdullahi Tukur