Aminiya:
2025-04-15@15:30:09 GMT

Rigima: Mawaƙi Portable ya kwana a hannun ’yan sanda

Published: 14th, April 2025 GMT

’Yan sanda sun kama shahararren mawaƙin zamani a Najeriya Habeeb Okikiola Badmus, wanda aka fi sani da Portable, bayan ƙazancewar rikicinsa da fitaccen ƙwararren mawakin Fuji, Okunola Saheed “Osupa.”

A ranar Lahadi da dare ne ’yan sanda daga Jihar Kwara suka yi takakkiya suka kamo Portable mai waƙar “Zazu Zeh” a garin Abeokuta, Jihar Ogun

Kakakin ’yan sanda na Jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ya ce an kama Portable bayan samun takardar ƙorafin da Osupa ya aike ɗauke da jerin manyan zarge-zarge da yake yi wa mawakin na “Zazu Zeh,” na ɓata suna, barazanar kisa, tunzura jama’a, zubar da da mutum da gangan, neman tayar da fitina, da kuma amfani da zagi da munanan kalamai.

“Saboda girman waɗannan zarge-zarge da kuma ingantattun shaidun da aka gabatar, rundunar ta samu sammacin kame daga Kotun Majiatare da ke zamanta a Ilorin, inda jami’anmu suka je Abeokuta, suka kamo wanda ake zargin suka kawo shi Ilorin domin ci gaba da bincike.”

Jami’in ya ce da kawo Portable jihar Kwara, nan take aka fara yi masa Portable tambayoyi da ɗaukar bayanansa a gaban lauyoyi daga bangarorin biyu.

Ya tabbatar da cewa Portable zai ci gaba da kasancewa a tsare kuma nan ba da komawa ba za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Rigimar mai zafi, tsakanin Portable da Osupa, ta samo asali ne daga rashin jituwa kan keta haƙƙin mallakar waƙa. Wannan rashin jituwa ta ɓarke ne a bainar jama’a lokacin da Portable ya yi amfani da zagi ga fitaccen mawakin na Fuji mai shekaru 55 a wani bidiyo da ya yaɗu, wanda ya jawo caccaka a kafafen sada zumunta.

A cikin bidiyo, Portable ya bayyana cewa, “Kuɗi ne ya jawo faɗan!” yana ƙoƙarin bayyana ɓacin ransa. Ya ce “Raina ya ɓaci ne saboda ina so a ba ni kuɗina, kuma na ji suna ƙoƙarin sauke waƙar.”

Bayan shan caccaka daga bisani ya saki wani bidiyo yana neman afuwar Osupa cikin girmamawa. Ya ce, “Sarki Saheed Osupa, babana, don Allah kada ka yi fushi. Ka ɗauke ni kamar ɗanka ka horar da ni.”

A wani yanayi mai ban mamaki kuma, Portable ya nuna cewa rigimar tasu wani salon neman magoya baya ne, har ma ya nemi a ba shi damar gudanar da wasanni. “Dukkanmu muna tallata kanmu… don Allah a ba ni aiki.”

Sai dai, Saheed Osupa ya yi watsi da neman afuwar a matsayin wanda bai isa ba, yana mai cewa dole Portable ya samu sakamakon abin da ya aikata.

Ƙi amincewar tasa ba ta yi wa Portable daɗi ba, har ya ƙi janyewa, inda a ƙarshe ya kai ga matakin da Osupa ya ɗauka na shigar da ƙara ga hukumar ’yan sanda.

Yanzu, duniyar nishaɗi ta zura ido tana kallon yadda za a ƙare a wannan rikici  manyan mawaka da ya tashi daga kafafen sada zumunta zuwa zauren kotu.

Shin Portable zai fuskanci cikakken hukuncin doka bisa ga zarge-zargen da ake yi masa, ko kuwa za a samu sasanci ne?

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: mawaki Mawaƙi Portable ya

এছাড়াও পড়ুন:

An yi garkuwa da masu ibada a Kogi

’Yan bindiga sun kai hari a kan taron masu ibada inda suka yi awon gaba da mutane da dama da ba a tantance ainihin yawansu ba.

Mutane suna tsaka da gudanar da ibadar dare ne a kan wani tsauni a lokacin da ’yan bindigar suka kai musu farmakin suka yi garkuwa da su.

Lamarin ya auku ne a ranar Juma’a yankin Egbola, a kan hanyar Agabja a Ƙaramar Hukumar Lokoja.

Shaidu sun bayyana cewa ’yan bangan gwmanatin jihar sun yi nasarar ceto wata mata daga cikin masu ibadan, bayan sun samu rahoton aukuwar lamarin.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato Yadda kisan mutum fiye da 50 a Filato ya tayar da ƙura

Wani ɗan banga daga cikin waɗanda suka kai ɗauki ya bayyana cewa matar ta tsere ne bayan da ’yan bindigar suka kawo harin, daga bisani ’yan bindigar suka tsince ta.

Wakilinmu ya yi ƙoƙarin yin magana da mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Kogi, ASP William Aya, amma jami’in bai amsa ko ɗaya daga cikin kiraye-kirayen wayan wakilin namu ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kano Za Ta Sake Buɗe Makarantun Kwana 10 Don Inganta Ilimin Yara Mata
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 109
  • An yi garkuwa da masu ibada a Kogi
  • Yaƙin Neman Zaɓe A 2027: Ƙungiya Ta Nemi A Maye Gurbin Mai Magana Da Yawun Shugaban Ƙasa
  • ‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A Adamawa
  • ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato
  • Gwamnatin Amurka Ta Yi Da’war Cewa; Ba Ta Neman Tashin Hankali Tsakaninta Da Iran
  • ’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara
  • Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis