‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Hada Makamai A Kano
Published: 14th, April 2025 GMT
Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta gano wani haramtaccen wurin hada makamai a jihar Kano, lamarin da ya kai ga kama wasu mutane uku tare da kwato bindigogi kirar gida guda 15 tare da harsashi 102. Wadanda ake zargin sun hada da Abdul Sadiq mai shekaru 43; Ahmad Muazu, 22; da Aliyu Sharif, mai shekaru 40, an kama su ne a ranar 10 ga watan Afrilu a unguwar Dorayi Babba da ke jihar, sakamakon wani hadin gwiwa da jami’an rundunar ‘yansandan jihar Kano suka jagoranta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kwamishinan ‘Yansandan Kano Ya Nemi Taimakon Sarakunan Gargajiya Wajen Kawo Ƙarshen Faɗan Daba
Ya ce sama da mutane 150 ne aka kama da laifin faɗan ɗaba da tashin hankali, tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi da kayan sata.
Ya ƙara da cewa matsalolin faɗan ɗaba da shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar jama’a da makomar matasa.
Duk da yake kame na da muhimmanci, Bakori ya ce dole ne a bai wa matasa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kuma wasu ayyuka da za su riƙa shagaltar da su zuwa hanya mafi dacewa.
Ya kuma shawarci shugabannin ‘yansanda na ƙananan hukumomi da su riƙa haɗa kai da sarakunan gargajiya da al’ummar yankinsu wajen gano matsalolin tsaro a yankunansu.
“Idan muka haɗa kai da goyon bayan jama’a, babu yadda ‘yan daba za su ci gaba da addabar Kano,” in ji CP Bakori.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp