Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran
Published: 14th, April 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran.
Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa: Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage.
Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan harkokin wajen Najeriya Ya kai ziyara Nijar
Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya jogoranci wata ziyarar aiki zuwa makobciyuar kasar Jamhuriyar Nijar.
Wannan it ace ziyara irinta ta farko da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai a Jamhuriyar Nijar tun bayan da sojoji karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani suka kifar da mulkin farar hula na Mohamed Bazoum a watan Yulin shekarar 2023.
Juyin mulkin da sojojin sukayi a Nijar ya haifar da takaddamar diflomasiyya sosai tsakanin Nijar da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta a wannan karon.
Batun mayar da hambararen shugaban Nijar Bazoum da kin lamuncewa juyin mulkin daga gwamnatin Najeriya da kuma kungiyar ta ECOWAS, shi ne a sahun gaba a takaddamar.
ECOWAS ta kakabawa Nijar tsauraren takunkumai tare kuma da yi mata barazanar daukan matakin soji idan sojojin basu mayar da Bazoum ba kan madafun iko.
Da alama dai wannan ziyarar ta ministan harkokin wajen Najeriyar zai yayafawa takun-sakar dake tsakanin kasashen makobtan juna masu raba iyaka da al’adu iri daya musamman a yankin arewacin Najeriya.