Aminiya:
2025-04-15@22:08:48 GMT

An rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Katsina

Published: 14th, April 2025 GMT

A wannan Litinin ɗin ce ne aka rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina waɗanda aka gudanar da zaɓensu a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025.

Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ne ya jagoranci rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin.

’Yar shekara 66 ta haifi ɗanta na 10 da kanta Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato

Sai dai gab da lokacin da za a rantsar da su, ɗaya daga cikinsu ya faɗi ya sume a lokacin da yake ƙoƙarin shiga rumfar da aka tanadar masu.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bakori Honarabil Aminu Ɗan Hamidu shi ne wanda ya faɗi kuma aka ɗauka ranga-ranga zuwa asibiti.

Binciken da muka yi ya nuna cewa, shugaban ya take wani sashe na babbar rigar shi ne ba tare da ya yi la’akari ba yayin da ya yunƙura da ƙarfi don hawa matattakalar shiga rumfar, lamarin da ya janyo rigar ta shaƙe shi ya faɗi a sume.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Katsina Ƙananan Hukumomi

এছাড়াও পড়ুন:

Mutane 2 Sun Rasu a Wajen Haƙar Ma’adinai A Jihar Neja

Rundunar ‘yansandan ta ce ta fara bincike kan lamarin, kuma ta ja kunnen jama’a da su guji irin wannan aiki da ya ke barazana ga rayuka, tsaro da tattalin arziƙin jihar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Kaduna ta Amince da Kudirin Kula da Lafiyar Kwakwalwa na Jihar
  • Mutane 2 Sun Rasu a Wajen Haƙar Ma’adinai A Jihar Neja
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato
  • Boko Haram ta kashe mutum 300 ta kwace ƙananan hukumomi 3 a Borno — Ndume
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno
  • An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo
  • NATE Ta Rantsarda Sabbin Shugabanni Reshen Jihar Kaduna
  • Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
  • Janar Tsiga, Mahaifiyar Rarara da muhimman mutane da aka sace a Katsina