Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa ta kama Umar Shaibu bisa zargin cin zarafin wata mata a yankin Jimeta a jihar. An kama Shaibu ne bayan wani bidiyo mai tayar da hankali ya yadu a kafafen sada zumunta, kamar yadda Jami’in hulda da Jama’a na ‘Yansandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana. Salamatu Yakubu, matar mai shekaru 22 daga Angwan Tana, an ce wanda ake zargin ya yi ma ta dukan jakin ne mai tsanani, Shaibu, wanda ake cewa shi ne dan uwanta.

Wannan lamarin ya janyo zarge-zargen daga al’umma da kuma kiran da aka yi wa Yansanda daga mutanen gari, da kungiyoyin fararen hula, da sauran masu rajin kare hakkin bil’adama domin a kama wanda ake zargi.

Ƴansanda Sun Kama  Ɓarayin Waya Masu Amfani Da Keke Napep A Adamawa An Kama Wanda Ake Zargi Da Kashe Mai PoS A Adamawa

An kama Shaibu ne tare da taimakon al’umma ta hanyar dabarun kula da tsaro na cikin gari. An tura matar da aka yi wa dukan cutar zuwa asibiti domin samun kulawar likita.

A halin yanzu, wanda ake zargin yana tsare a sashin binciken laifuka na musamman na Jihar (SCID) a sashin kula da mata domin a gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu. Rundunar Yansandan ta tabbatar wa da jama’a cewa za a binciki lamarin sosai kuma wanda ake zargi zai fuskanci shari’a bisa dokokin da suka dace.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Adamawa

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu ta tsare ’yan TikTok 2 a Kano

Wata Kotun Majistire mai lamba 7 a Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu ’yan TikTok biyu kan zargin wallafa wasu bidiyon batsa a shafukansu na dandalin sada zumunta.

Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ce ta gurfanar da ababen zargin biyu — Isa Kabir Brigade da Fatima Adam Kurna — kan wallafa bidiyon da suka saɓa wa tarbiyya da addini.

An rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Katsina ’Yar shekara 66 ta haifi ɗanta na 10 da kanta

Sai dai bayan lauyan da ke ɓangaren masu shigar da ƙara, Garzali Maigari Bichi ya karanta musu ƙunshin tuhume-tuhumen, sun musanta wasu daga ciki.

Dangane da hakan ne Alƙalin Kotun, Halima Wali ta bayar da umarnin tsare ababen zargin tare da ɗage zaman kotun zuwa ranar 24 ga watan Afrilu.

Ana iya tuna cewa dai Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ta ɗaura ɗamarar tsaftace dandalan sada zumunta ta hanyar kame da ladabtar da masu wallafe-wallafen duk wani abu da ya ci karo da tarbiyya da addini.

Ko a bayan nan sai da hukumar ta gurfanar da wasu mutum biyu — waɗanda aka yankewa hukuncin ɗauri na shekara guda ko zaɓin biyan tara ta Naira dubu 100 — kan wallafa bidiyon batsa a shafukansu na TikTok.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • EFCC ta gaza tabbatar da tuhumar Murja kan zargin wulaƙanta takardar Naira
  • Gwamnatin Kano Za Ta Sake Buɗe Makarantun Kwana 10 Don Inganta Ilimin Yara Mata
  • Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 ta jikkata 69 a awa 24 a Gaza
  • Sojoji sun kama ’yan bindiga 12 a Nijar
  • Kotu ta tsare ’yan TikTok 2 a Kano
  • ‘Yansanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Ɓarayin Wayar Wutar Lantarki Ne A Yobe
  • ‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Hada Makamai A Kano
  • An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo
  • Amnesty Ta Zargi  Rundunar “RSF” Ta Sudan Da Cin Zarafin Mata