Wata Kotun Majistire mai lamba 7 a Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu ’yan TikTok biyu kan zargin wallafa wasu bidiyon batsa a shafukansu na dandalin sada zumunta.
Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ce ta gurfanar da ababen zargin biyu — Isa Kabir Brigade da Fatima Adam Kurna — kan wallafa bidiyon da suka saɓa wa tarbiyya da addini.
Sai dai bayan lauyan da ke ɓangaren masu shigar da ƙara, Garzali Maigari Bichi ya karanta musu ƙunshin tuhume-tuhumen, sun musanta wasu daga ciki.
Dangane da hakan ne Alƙalin Kotun, Halima Wali ta bayar da umarnin tsare ababen zargin tare da ɗage zaman kotun zuwa ranar 24 ga watan Afrilu.
Ana iya tuna cewa dai Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ta ɗaura ɗamarar tsaftace dandalan sada zumunta ta hanyar kame da ladabtar da masu wallafe-wallafen duk wani abu da ya ci karo da tarbiyya da addini.
Ko a bayan nan sai da hukumar ta gurfanar da wasu mutum biyu — waɗanda aka yankewa hukuncin ɗauri na shekara guda ko zaɓin biyan tara ta Naira dubu 100 — kan wallafa bidiyon batsa a shafukansu na TikTok.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
EFCC ta gaza tabbatar da tuhumar Murja kan zargin wulaƙanta takardar Naira
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, ta gaza tabbatar da zargin wulaƙanta takardar Naira da take yi wa fitacciyar ’yar TikTok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya.
A bayan nan ne EFCC ta gurfanar da Murja a gaban kotu kan zargin cewa ta ci karo da wani bidiyonta tana rawa a kan takardun kuɗi har kimanin Naira dubu 400.
A ƙunshin ƙarar da EFCC ta gabatar mai lamba FHC/KN/CS/18/2025 a gaban wata Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano, ta ce laifin da take tuhumar Murja tanadi na Kundin Dokokin Babban Bankin Nijeriya CBN wanda ya haramta wulaƙanta takardar Naira ta kowace siga.