Iran, Iraki Sun Karfafa Dangantakar Makamashi
Published: 14th, April 2025 GMT
Kasashen Iran da kuma Iraki sun kudiri anniyar karfafa alaka ta fuskar makamashi.
A ganawar da suka yi a birnin Bagadaza, kasashen biyu sun jaddada fadada hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin mai da iskar gas, inda kasar Irakin ta bayyana matukar sha’awar yin hadin gwiwa a fannin fasaha da zuba jari da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Taron ya yi nuni da karfafa huldar dabarun samar da makamashi tsakanin kasashe biyu masu makwabtaka da juna.
Mataimakin firaministan kasar Iraki mai kula da harkokin makamashi Hayan Abdul-Ghani Al-Sawad ya bayyana cewa, Iraki na ci gaba da gudanar da ayyukan da ke da nufin cimma dogaro da kai wajen samar da albarkatun man fetur.
Ya jaddada aniyar Bagadaza na fadada hadin gwiwar fasaha da kuma jawo hannun jarin Iran a bangaren makamashi na Iraki.
Iraki na da burin rage dogaro da man fetur da ake shigowa da su daga kasashen waje kuma tana kallon Iran a matsayin babbar abokiyar huldar cimma wannan buri saboda ci gaban da take da shi na tace man.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Da Prabowo Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 75 Da Kulla Huldar Diplomasiyya Tsakanin Sin Da Indonesiya
A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Indonesia, Prabowo Subianto suka yi musayar taya juna murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Inda shugaba Xi ya ce, yana dora matukar muhimmanci kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Indonesia, kuma a shirye yake ya yi amfani da bikin cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, a matsayin wata dama ta yin aiki tare da shugaba Prabowo, wajen kara zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da karfafa hadin gwiwa a batutuwan da suka shafi bangarori daban daban bisa manyan tsare-tsare, da ci gaba da inganta al’ummar Sin da Indonesiya mai kyakkyawar makomar bai daya daga dukkan fannoni, kuma bisa yanayin sabon zamani, da kafa misali na hadin kai da amincewa da juna tsakanin manyan kasashe masu tasowa, da zama abin koyi na ci gaban hadin gwiwar bai daya ga kasashe masu tasowa, ta yadda za su ba da gudummawa tare wajen ci gaban dan Adam.
A nasa bangaren, Prabowo ya bayyana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da zurfafa hadin gwiwa tare da tabbatar da zumunci a tsakanin al’ummomin kasashen biyu, ta yadda za su ba da gudummawa mai kyau ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp