Aljeriya ta yi barazanar korar jami’an diflomasiyyar Faransa 12
Published: 14th, April 2025 GMT
Rikicin diflomasiyya tsakanin Paris da Algiers na dada kamari, inda Aljeriya ta bukaci wasu jami’an diflomasiyyar Faransa 12 da su fice daga kasar cikin sa’o’i 48.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya sanar cewa, Aljeriya ta bukaci jami’an diflomasiyyar Faransa da su fice daga kasar bayan kama wasu ‘yan kasar Aljeriya uku a Faransa.
“Ina kira ga hukumomin Aljeriya da su yi watsi da wannan matakin, inda ya kara da cewa: “Idan har aka ci gaba da yanke shawarar korar wakilanmu, ba mu da wani zabi illa mu mayar da martani cikin gaggawa.”
Shekaru da dama, alakar diflomatoyyar da ke tsakanin Aljeriya da Faransa ta yi tsami.
A farkon watan Afrilu, ministan harkokin wajen Faransa ya je kasar Aljeriya, domin kokarin warware matsalolin da suka jefa kasashen biyu cikin tabarbarewar diflomasiyya.
Bayan ganawa da shugaban kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, Jean-Noël Barrot ya bayyana muradin kasashen biyu na “sake gina dangantakar abokantaka.”
A daidai lokacin da ake fuskantar tsamin dangantaka tsakanin Algiers da Paris, ofishin mai gabatar da kara na Faransa ya tuhumi, wasu ‘yan kasar Aljeriya uku, a ranar 11 ga Afrilu, ciki har da wani jami’in ofishin jakadanci, da zarginsu da hannu a sace wani dan adawar gwamnatin Algeria, Amir Boukhors, da aka sani da “AmirDZ na Paris” a cikin 2024.
Aljeriya ta yi kakkausar suka a ranar Asabar, 12 ga Afrilu, don nuna adawa da kamawa da tsare daya daga cikin jami’an ofishin jakadancinta a kasar Faransa tare da neman a gaggauta sakin shi.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Aljeriya Aljeriya ta
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Isa Kuala Lumpur Domin Ziyarar Aiki A Malaysia
A yammacin yau ranar 15 ga watan Afrilu ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Kuala Lumpur ta jirgin sama na musamman, domin gudanar da ziyarar aiki a kasar Malaysia.
Xi Jinping ya gabatar da rubutacciyar jawabi a filin tashi da saukar jiragen sama, inda ya ce, yana fatan daukar wannan ziyara a matsayin wata dama ta kara zurfafa dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, da kara amincewa da juna a fannin siyasa a tsakanin bangarorin biyu, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a fannin ayyukan zamanantarwa, da sa kaimi ga yin mu’amala da fahimtar juna a tsakanin al’ummomi, da inganta gina al’umma mai kyakkaywar makomar bai daya tsakanin Sin da Malaysia zuwa wani sabon mataki. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp