HausaTv:
2025-04-15@23:58:07 GMT

Daruruwan ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Masallacin Kudus

Published: 15th, April 2025 GMT

A jiya Litinin daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus, suna masu bayar da take na tsokana ga Musulmi. Har ila yau ‘yan share wuri zauna din sun kuma gudanar da na’u’oin ibadu na addinin yahudanci a cikin farfajiyar masallacin na Kudus.

Ma’aikatar  da take kula da wuraren ‘wakafi’ na musulunci, ta bayyana cewa; Adadin yahudawa ‘yan share wuri zauna din da su ka kutsa cikin masallacin na Kudus sun kai 765,kuma ‘yan sanda sun rika yi musu rakiya.

A lokaci daya kuma jami’an tsaron na ‘yan sahayoniya sun tsaurara matakan kuntatawa Falasdinawa masu shiga cikin masallacin na Kudus domin yin salla.

Wannan tsokanar ta ‘yan share wuri zauna a masallacin Kudus, tana faruwa ne a lokacin da a can yammacin kogin Jordan, yahudawan suke lalata gonakin Falasdinawa da kankare kasar gonakin ta hanyar amfani da manyan motoci na buldoza.

Har ila yau ‘yan sandan HKI sun kutsa cikin garuruwa da dama na Falasdinawa a yammacin kogin Jordan, inda su ka kama mutane da dama. Haka nan kuma sanadiyyar  harbe-harebn da su  ka yi, sun jikkata Falasdinawa 4 a sansanin Jalzuna dake arewacin birnin Ramallah.

A birnin Tubas kuwa ‘yan sahayoniyar sun kutsa cikin unguwanni mabanbanta tare da tilastawa mazauna wasu unguwanni da su fice daga cikin gidajensu. Kwamitin al’umma na Falasdinu a yankin ya sanar da cewa  a tsawon lokacin yaki adadin Falasdinawan da aka tilastawa ficewa daga cikin gidajensu, sun kai dubu 3 da 227.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: yan share wuri zauna

এছাড়াও পড়ুন:

Rundunar “Gulani” Ta Shiga Sahun Masu Kin Amincewa Da Yaki

A kalla tsoffin sojojin rundunar “Gulani” ta HKI 150 ne su ka rattaba hannu akan takardar yin kira da a dawo da fursunoni gida daga Gaza.

Ita dai rundunar “Gulani” ce mafi karf a tsakanin rudunonin sojan HKI,kuma tun da aka kafa ta, ta shiga dukkanin yake-yaken da HKI ta yi.

Wadanda su ka rattaba hannu akan wasikar sun bayyana goyon bayansu ga wasikar da sojan sama su ka rubuta a ranar 9 ga watan Aprilu da ake ciki,ko da kuwa sakamakon hakan shi ne kawo karshen yaki.

A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,dubban sojojin HKI sun rattaba hannu akan wasika wacce take yin kira da a kawo karshen yakin Gaza da kuma dawo da fursunonin da suke can.

A ranar juma’ar da ta gabata kafafen watsa labaru HKI sun ambaci cewa, da akwai sojojin bayan fage 1000 da su ka rattaba hannu akan wasika, da kuma tsofaffin sojojin soja a tsakaninsu da akwai wadanda suna kan ganiyar aikinsu.

Bayan wannan ne kuma sojojin dake kula da motocin yaki da tankoki su 15,25 su ka bi bayansu, sai kuma wasu tsoffin sojojin sama Jannati ,haka nan kuma sojan ruwa da likitocin soja 100. A cikin kwanaki  kadan da su ka gabata ma dai wasu jami’an daga cikin tsoffin ma’aikatan kungiyar leken asirin soja sun shiga cikin masu rubuta wasikar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Samarwa Matasa Abun Yi Shi Zai Kawo Ƙarshen Ta’addancin Boko Haram Da ‘Yan Bindiga – Zulum 
  • Lauyoyin London Suna Tattara Bayanai Kan ‘Yan Birtaniya Da Suka Yi  Yaki Cikin Sahun Yahudawan Sahayoniyya A Gaza
  • Rundunar “Gulani” Ta Shiga Sahun Masu Kin Amincewa Da Yaki
  •  Aljeriya Ta Kori Jami’an Diflomasiyya Faransa 12
  • ‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A Adamawa
  • ‘Yansanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Ɓarayin Wayar Wutar Lantarki Ne A Yobe
  • ‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Hada Makamai A Kano
  • Hukumar OCHA Ta Bayyana Cewa Yahudawan Sahyoniyya Sun Ninninka Ayyukan Korar Falasdinawa A Yamma Da Kogin Jordan
  • ’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara