Matashi ya yi yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a Kano
Published: 15th, April 2025 GMT
Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari kan laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a unguwar Fagge da ke Jihar Kano.
Kotun da ke zamanta a yankin Mai Alluna ta yanke wa matashin hukuncin ne bayan bayan alƙali ya kama shi da laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa almakashi saboda ya hana shi kuɗin kashewa.
’Yan sanda sun gurfanar da matashin ne a kan laifin ɗura ashariya da barazanar kisa da kuma ɗaukar makami ba bisa ka’ida ba.
Bayan karanta masa takardar tuhumar, matashin ya amsa laifin, inda Alƙali Nasir Ahmad ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyu da tarar Naira dubu 20, da kuma karin ɗaurin wata shida tare da bulala 40.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Sanar Da Kasar Oman A Matsayin Wajen Tattaunawa Na Gaba Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa: Za a gudanar da zaman tattaunawa kan Shirin makamashin nukuliyar Iran zagaye na biyu ne a birnin Muscat na kasar Oman
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Zaman tattaunawa zageye na biyu wanda ba na kai tsaye ba, tsakanin Iran da Amurka zai kasance ne a birnin Muscat fadar mulkin kasar Oman.
Baghaei ya yi watsi da rade-radin da ake yi kan inda za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar kai tsaye tsakanin Iran da Amurka, Baghaei ya ce, “Bayan tuntubar juna, an yanke shawarar cewa birnin Muscat ne zai karbi bakwancin zagaye na biyu na shawarwarin, wanda za a yi a ranar Asabar mai zuwa.”
Wani abin lura a nan shi ne, an gudanar da shawarwari ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka a ranar Asabar tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da manzon Amurka na musamman kan yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff dangane da batun Shirin makamashin nukiliyar Iran da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata na rashin adalci da baya kan tubalin ka’ida. Tattaunawar ta samu halartar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i da mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin siyasa Majid Takht-e Ravanchi, da mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da na kasa da kasa Kazem Gharibabadi, da manyan masu shiga tsakani kan batun dage takunkumi da batun Shirin makamashin nukiliya, da kuma kwararrun da suka dace.