Ministan Harkokin Noma Na Kasar Iran Ya Kama Hanya Zuwa Kasar Brazil
Published: 15th, April 2025 GMT
Ministan harkokin noma na JMI Ghulan Reza Noori Ghezelji ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatin kasar zuwa kasar Brazil don halattan taron ministocin noma na kungiyar BRICS da kuma tattauna al-amura masu muhimmanci wadanda suka shafi ayyukan noma a duniya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta fara aiki a matsayin mamba a kungiyar raya tattalin arziki na kasashen BRICS, wacce ta zama cikekken maba a farkon wannan shekara.
Ta fara aiki tare da sauran kasashen kungiyar wadanda suka kafa ta, wato Brazil, Rasha, India, China,da kuma Afirka ta kudu..
Halattar wannan taron ba kawai zai kara karfin JMI a cikin kungiyar BRICS ba, sai dai zai kara inganta matsayin kasar a fagen noma da abinda ya shafi noma a duniya. Taron na Brazil zai maida hankali kan aminci samun abinci ga yan kasashen kungiyar da kasuwancinsa a duniya. Da kuma hanyoyin samar da samar da kudade don ayyukan noma duniya.
Daga karshe taron na Brazil zai bayyana jadawalin ayyukan kungiyar dangane da noma a shekara ta 2025.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
Tsangayar Ilimi na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ya shirya wani taron bikin cika shekaru 50 da kafuwa tare da gudanar da taron kasa karo na uku.
Taron wanda aka yi wa take da “Ilimi Mai Sauya Rayuwa Don Gaba: Fuskantar Sabbin Kalubale da Buɗe Damar Samun Ci gaba” ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki daga sashen ilimi.
Da take jawabi a wajen taron, Minista a ma’aikatar Ilimi Farfesa Suwaiba Ahmed Sa’id ta bayyana cewa, a ƙoƙarin da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ke yi na ƙarfafa tsarin ilimi, ya amince da kashe Naira biliyan 120 don bunƙasa shirin fasaha da koyon sana’o’i (TVET) a Najeriya.
Ministar ta kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Naira biliyan 40 domin kammala aikin ɗakin karatu na ƙasa da aka yi watsi da shi, domin tallafawa bincike da cigaban karatu.
Farfesa Suwaiba ta ƙara da cewa, ma’aikatar ilimi ta tarayya ƙarƙashin jagorancin Minista Alausa ta ƙaddamar da Shirin Sabunta Hanyar Ilimi ta Najeriya (NESRI).
“Ina da burin mayar da Najeriya daga tattalin arzikin da ke dogara da albarkatu zuwa tattalin arzikin da ke dogara da ilimi, tare da rage yawan yara da ba sa zuwa makaranta, rage ƙarancin koyo, da samun ƙara ƙwarewa.”
Yayin da yake buɗe taron, Shugaban Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana nasarorin da sashen ya samu, inda ya ce ya samar da manyan mutane kamar ministocin ilimi biyu, shugabannin jami’o’i tara, da matan gwamnan jihar Kano guda uku, da sauran fitattun ’yan Najeriya da suka yi fice a fannoni daban-daban.
Yayin da yake yabawa taken taron da dacewarsa, Farfesa Sagir ya tabbatar da cewa jami’ar tana nan daram wajen tallafawa duk wani shiri da zai ɗaga matsayin ilimi zuwa na ƙasa da ƙasa.
A jawabinsa na maraba, Shugaban tsangayar Ilimi na Jami’ar Bayero Kano (BUK), Dakta Abubakar Ibrahim Hassan, ya jaddada yadda tsangayar ke kokari wajen shirya harkokin ilimi da na kimiyya.
“Daga cikin nasarorin da Jami’ar BUK ta samu a kwanan nan akwai samun tallafin TETFUND guda biyu da kowanne ya haura naira biliyan 30, tare da lashe wani shirin koyar da harsuna biyu wanda Bankin Raya Musulunci da Hukumar Ilimin Firamare ta Kasa (UBEC) suka dauki nauyi.”
Taron ya yi armashi inda aka bayar da lambar yabo ga fitattun ‘yan Najeriya da suka hada da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa Farfesa Hafsat, da Minista a ma’aikatar Ilimi ta Jiha Farfesa Suwaiba, tsohuwar Ministar Ilimi Farfesa Rukayya, da Farfesa Isah Yahaya Bunkure da wasu da dama.
Daga Khadija Aliyu