Hauhawar Farashi ya ƙaru a watan Maris — NBS
Published: 15th, April 2025 GMT
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce hauhawar farashi ya ƙaru a ƙasar zuwa kashi 24.23 cikin 100 a watan Maris.
Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna an samu ƙarin kashi 1.05 daga kashi 23.18 cikin ɗari da aka samu a watan Fabrairu.
EFCC ta gaza tabbatar da tuhumar Murja kan zargin wulaƙanta takardun kuɗi ’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin TarayyaWannan ne karon farko da aka samu ƙarin hauhawar farashin tun bayan da hukumar ta NBS ta soma fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi a farkon shekarar nan.
Sai dai bayan soma amfanin da sabon tsarin fitar da ƙididdigar a watan jiya, NBS ta ce da wuya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu.
A wani jawabi da ya yi manema labarai tun a watan da ya gabata, shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya bayyana cewa sun sauya tsarin ne saboda “daidaita shi da irin na sauran ƙasashen duniya.”
Ya ce karo na ƙarshe da Nijeriya ta sauya tsarin ƙididdigar shi ne a shekarar 2009, inda ake ƙididdige farashin kayan da aka fi amfani da su a wannan tsakanin.
Hakan na nufin yanzu za a riƙa kwatanta farashin kayayyakin da aka ƙididdige daga shekarar 2024, maimakon 2009 da aka riƙa amfani da ita a baya.
A sabbin alƙaluman da NBS ta fitar, ta alaƙanta hauhawar farashin da tashin kayayyaki irinsu citta, garin rogo, shinkafa, zuma, dankali, barkono da sauransu.
Aminiya ta ruwaito cewa, Hukumar NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hauhawar Farashi Maris Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Cinikin Waje Na Sin Ya Karu Da Kashi 1.3 A Rubu’in Farkon Bana
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp