Zulum ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su maida hankali wajen samar da damammaki ga matasa a arewacin Nijeriya.

 

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa, taron da aka yi a Jihar Borno an yi shi ne domin karfafa hadin kan jihohin Arewa da kuma tattaunawa kan halin da yankin ke ciki domin tallafa wa shugabannin siyasa wajen magance matsalolin da ke addabar Arewa.

 

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) da babban hafsan tsaro (CDS) da babban sufeton ‘yansanda (IGP) duk sun samu wakilci a taron sarakunan.

 

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Mohammed Inuwa Yahaya, wanda mataimakinsa, Manassa Daniel Jatau ya wakilta; Sanata Kaka Shehu Lawan; Shehun Borno, Abubakar Umar Garbai, da sauran sarakunan gargajiya da dama a fadin jihohin Arewa 19.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zullumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar.

Waɗannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da iƙirarin hwamnati cewa an yi nasarar nakasa ƙungiyar.

Ko mene ne dalilin sake farfaɗowar ƙungiyar ta Boko Haram a wannan lokaci?

NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’

Wannan ne batun shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16971864-dalilan-farfa-owar-boko-haram-a-jihar-borno.mp3?download=true

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gazawar Gwamnati Kan Kiyaye Rayuka Da Dukiyoyi: Gwamnan Filato Ya Nemi Yafiyar Al’ummar Jihar
  • HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno
  • Kwamishinan ‘Yansandan Kano Ya Nemi Taimakon Sarakunan Gargajiya Wajen Kawo Ƙarshen Faɗan Daba
  • Kwamishinan ‘Yansandan Kano Ya Nemi Taimakon Sarakunan Gargajiya Wajen Kawo Ƙarshen Faɗan Daba A Jihar
  • Boko Haram ta kashe mutum 300 ta kwace ƙananan hukumomi 3 a Borno — Ndume
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Abincin karnuka ya fi namu —Fursunonin Najeriya
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno
  • Zulum Ya Gana Da Yaron Da Aka Ci Zarafi, Ya Ba Shi Gida, Tallafin Karatu