Aminiya:
2025-04-16@11:03:24 GMT

Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da Litinin

Published: 16th, April 2025 GMT

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 18, da kuma Litinin, 21 ga watan Afrilun 2025 a matsayin ranakun hutun bikin Easter a faɗin ƙasar.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Barcelona da PSG sun tsallaka zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo

A jawabin da Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida , Dokta Magdalene Ajani ta fitar, Ministan ya nemi mabiya addinin Kirista su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasar addu’o’in zaman lafiya da haɗin kai.

Yayin da yake taya mabiya addinin Kirista murnar wannan lokaci, Mista Tunji yana kuma kira ga al’ummar Nijeriya da su haɗa hannu da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a ƙoƙarin da take yi na inganta rayuwar al’umma ta hanyar ci gaban ƙasa.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya

’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi.

Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya.

Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje.

Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin a fito da ita, shi ya sa ingancin ya samu matsala.

Duk da samun koma baya: Najeriya ce kasa mafi arzikin danyen mai a Afirka —OPEC Matashi ya yi yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a Kano

Don haka ya shawarci masu saya da su shanya ta a rana kuma su wanke ta sosai sa’annan su dan turara ta domin dawo da ingancinta.

A gefe guda kuma wadanda da suka amfana da wani rukuni na daban na shinkafar gwamnatin sun yaba da ingancinta ta fuskar dandano da kuma yanayi.

Kawo yanzu dai hukumomi ba su ce uffan game da korafin da jama’a ke yi kan wannan lamari ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Ta Ayyana 18 Da 21 Ga Afrilu A Matsayin Hutun Esta
  • DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo
  • Minista Ya Gargaɗi Jami’an Gwamnati Kan Rashin Sanin Ilimin Tantance Ingantattun Labarai
  • Budurwar da ke rayuwa a banɗaki don gudun biyan kuɗin hayar gida
  • ’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Zanta Da Tokwaransa Na Kasar Kuwait
  • Ministan Harkokin Noma Na Kasar Iran Ya Kama Hanya Zuwa Kasar Brazil
  • Babban Daraktan Hukumar IAEA, Zai Ziyarci Iran ranar Laraba
  • Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken Tinubu