Aminiya:
2025-04-16@14:30:24 GMT

Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Peru ɗaurin shekaru 15

Published: 16th, April 2025 GMT

An yanke wa tsohon shugabar ƙasar Peru, Ollanta Humala hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari.

Wata kotu a ƙasar ce ta yanke masa hukuncin bisa samunsa da laifin halatta kuɗin haram a badaƙalar cin hanci da katafaren kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht ke yi don samun kwangila.

Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da Litinin

Haka kuma, ita ma mai ɗakinsa, Nadine Heredia, an yanke mata makamancin wannan hukuncin, duk da cewa ba ta halarci zaman kotun ba, saboda haka alƙalin ya bayar da umarnin kamo ta.

Ollanta Humala, mai shekaru 62, ya kasance tsohon shugaban ƙasar Peru na biyu da aka samu da laifi, lamarin da ya sa nan take aka kai shi wani gidan yari da ke gabashin Lima, inda ake tsare da tsoffin shugabannin kasar Peru Alejandro Toledo da Pedro Castillo.

Wannan hukuncin na zuwa ne sama da shekaru uku da fara shari’ar Humala wanda ya mulki ƙasar Peru daga 2011 zuwa 2016 —amma dai lauyoyinsa sun bayanna cewa za su ɗaukaka ƙara.

Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce Kamfanin Odebrecht ya ba da cin hanci dala miliyan 788 a cikin shekaru goma ga gwamnatocin yankin Latin Amurka domin samun kwangilar gine-gine.

Kamfanin ya bayyana cewar ya bayar da dala miliyan 29 na cin hanci ga Peru a tsakanin 2005 da 2014.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu Ta Tsare Matasa 2 Kan Wallafa Bidiyon Batsa A TikTok A Kano

Hukumar tace fina-finai na ci gaba da yaƙi da duk wani abu da ya saɓa da tarbiyya da addini a kafafen sada zumunta a Jihar Kano.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ina Da Ƙwarewar Da Zan Iya Zama Shugaban Ƙasar Nijeriya – Makinde
  • Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Peru ɗaurin shekaru 15 kan laifin rashawa
  • JAN KUNNE: Ɗan Atiku Abubakar ya mayar wa ɗan gwamnan Bauchi zazzafan martani
  • Ana barazanar korar sojojin Isra’ila da ke neman a kawo ƙarshen yaƙin Gaza
  • An Yanke Masa Hukuncin Ɗaurin shekaru 2 A Gidan Yari Saboda Yunƙurin Daɓa Wa Mahaifinsa Almakashi A Kano
  • CMG Ta Kulla Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Da Gidan Talabijin Na Kasar Vietnam
  • Kotu Ta Tsare Matasa 2 Kan Wallafa Bidiyon Batsa A TikTok A Kano
  • Matashi ya yi yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a Kano
  • Jiragen Saman Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Luguden Wuta Kan Asibitin Baptist Da Ke Gaza