Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Peru ɗaurin shekaru 15 kan laifin rashawa
Published: 16th, April 2025 GMT
An yanke wa tsohon shugabar ƙasar Peru, Ollanta Humala hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari.
Wata kotu a ƙasar ce ta yanke masa hukuncin bisa samunsa da laifin halatta kuɗin haram a badaƙalar cin hanci da katafaren kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht ke yi don samun kwangila.
Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Juma’a da LitininHaka kuma, ita ma mai ɗakinsa, Nadine Heredia, an yanke mata makamancin wannan hukuncin, duk da cewa ba ta halarci zaman kotun ba, saboda haka alƙalin ya bayar da umarnin kamo ta.
Ollanta Humala, mai shekaru 62, ya kasance tsohon shugaban ƙasar Peru na biyu da aka samu da laifi, lamarin da ya sa nan take aka kai shi wani gidan yari da ke gabashin Lima, inda ake tsare da tsoffin shugabannin kasar Peru Alejandro Toledo da Pedro Castillo.
Wannan hukuncin na zuwa ne sama da shekaru uku da fara shari’ar Humala wanda ya mulki ƙasar Peru daga 2011 zuwa 2016 —amma dai lauyoyinsa sun bayanna cewa za su ɗaukaka ƙara.
Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce Kamfanin Odebrecht ya ba da cin hanci dala miliyan 788 a cikin shekaru goma ga gwamnatocin yankin Latin Amurka domin samun kwangilar gine-gine.
Kamfanin ya bayyana cewar ya bayar da dala miliyan 29 na cin hanci ga Peru a tsakanin 2005 da 2014.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sabon Shugaban Kasar Gabon Ya Bayyana Shiransa Na Kawo Sauyi Mai Kyau A kasar
Bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta tabbatar da nasarar da Brice Oligui yayi a zaben shugaban kasa na karshen makon da ya gabata, shugaban ya gabatar da jawabinsa na farko ga mutanen kasar, inda ya bayyana masu kan cewa, babu jin dadi sai tare da wahala.
Shafin tanar gizo na labarai ‘Africa News” ya nakalto shugaban yana cewa muhimman al-amuran da zai sa a gaban a shugabancin kasar sun hada da sauya tsarin tattalin arzikin kasar daga dogaro da man fetur zuwa harkokin kasuwanci, har’ila yau zai yaki cin hanci da rashawa.
Brice ya ce, ya zo ne a matsayin mai gina kasa, kuma yana son taimakon su don samun nasara a wannan gagarum,in aikin.
A ranar lahadin da ta gabata ce hukumar zaben kasar Gabaon ta bada sakamakon zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a ranar Asabar wanda ya nuna cewa masu zabe a kasar sun zabi Brice a matsayin shugaban kasa tare da samun kasha 90.4% na yawan kuri’un da aka kada, kuma yawan mutanen da suka fito kara kuri’un ya kai kasha 74%.