HausaTv:
2025-04-18@23:13:10 GMT

 ‘Yan Hamayyar Tanzaniya Sun Ki Amincewa Da Hana Su Shiga Zabe

Published: 16th, April 2025 GMT

Jam’iyyar Hamayyar siyasa ta “Chadema” a kasar Tanzania ta ki amincewa da matakin gwamnatin kasar na haramta mata shiga manyan zabukan da za a yi a watan Oktoba.

Hukumar zaben kasar ta Tanzania ta zargi jam’iyyar Chameda’ da cewa ta ki amincewa ta rattaba hannu akan dokokin zabe, tana mai yin kira gare ta da ta girmama hukumar zaben kasar.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai babbar jam’iyyar adawa ta kasar Tanzania ta kauracewa halartar taron da aka yi wanda ya kunshi dukkanin jam’iyyun siyasa da su ka rattaba hannu akan dokokin zabe. Rattaba hannu akan dokokin dai yana a matsayin daya daga cikin sharuddan shiga cikin zabe da jam’iyyu za su yi,kamar yadda Ramadhani Kalima, daraktan hukumar zaben kasar ya fada wa manema labaru.

Sai dai kuma sakataren jam’iyyar Chadema  Regemeleza Nshala  ya bayyana matakin na  hukumar zaben da cewa ya saba wa doka. Haka nan kuma ya kara da cewa,abinda doka ta ce, duk jam’iyyar da ba ta rattaba hannu akan dokoki za a ci tararshi, ba hana shi shiga zabe ba.

An kama shugaban jam’iyyar ta Chameda,Tundu Lissu a yayin da ya shiga cikin zanga-zangar da take yin kira da a sauya dokokin zabe kafin lokacin zaben ya zo.

Jami’an ‘yan sanda sun yi awon gaba da shugaban jam’iyyar ta adawa, an kuma zarge shi da cin amanar kasa.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun zargi gwamnatin kasar ta Tanzania da amfani da dabaru mabanbanta  na cutar da jam’iyyar ta jam’iyyar adawa. Gwamnatin kasar ta Tanzania ta yi watsi da zargin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An Kashe Mutane 7 A Yayin Da ‘Yan Ta’adda Suka Ƙaddamar Da Wani Sabon Hari A Adamawa

An tabbatar da mutuwar mutane bakwai a wani sabon harin da ‘yan ta’adda suka kai a kauyen Garaha Lar da ke jihar Adamawa. Shugaban karamar hukumar Hong, Honarabul Usman Wa’aganda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa, wani mazaunin garin ya ɓata yayin da maharan suka lalata gidaje da kadarori. An Gudanar Da Harkokin Cudanya Da Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Malaysia A Birnin Kuala Lumpur  Jigawa Za Ta Zama Cibiyar Binciken Lafiya Nan Ba Da Jimawa Ba – Gwamna Namadi Wa’aganda ya kuma bayyana cewa, wani Ɗan banga na yankin ya mutu bayan da wani bam ya tashi a lokacin da yake ƙoƙarin tabbatar da tsaron yankin. A cewarsa, motar ‘yansandan da ke sintiri ta ofishin ‘yansanda na Garaha ita ma ta ƙone yayin da wani abun  fashewa ya fashe acikin motar amma babu wani mutum da ya rasa ransa. Shugaban ya ce, tsoron bama-baman da maharan ke amfani da su ya sanya zuwa wuraren da aka kai hare-haren ke da matukar wuya. Wa’aganda ya buƙaci a tura sojoji yankin da kuma tallafa wa waɗanda harin ya rutsa da su.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fani-Kayode ya zargi Isra’ila da Hannu a tashe-tashen hankula a Najeriya
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Iyayen Sanata Natasha A Kogi
  • Gwamnatin Sakkwato Ta Siyawa ‘Yan Gudun Hijira Gidan Miliyan 100
  • Kasar Pakistan Ta Kara Jaddada Dokar Rashin Amincewa Da HKI A Matsayi Kasa
  • MDD Ta Nuna Damuwarta Akan Kokarin Sake Raba Kasar Sudan Gida Biyu
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 157, Sun Ƙwato Bindigu Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano
  • An Kashe Mutane 7 A Yayin Da ‘Yan Ta’adda Suka Ƙaddamar Da Wani Sabon Hari A Adamawa
  • ‘Yan Ta’adda Sun Tarwasta Gadar Mandafuma A Jihar Borno
  • Matashin Da Ya Ƙware Wajen Kashe Mutane Da Ƙwace Ya Miƙa Kansa Ga ‘Yansanda A Kano