Yadiot Ahranot: Amurka Ta Bayyana Lokacin Ficewarta Daga Syria
Published: 16th, April 2025 GMT
Jaridar “Yadiot-Ahranot” ta rubuta cewa, jami’an Amurka sun sanar da sojojin Isra’ila a lokacin da za ta janye sojojinta daga kasar Syria.
Jaridar ta ce, jami’an tsaron kasar ta Amurka sun fada wa sojojin Isra’ila cewa, janye sojojin nata zai fara ne nan da watanni biyu masu zuwa.
Rahoton jaridar ta ‘yan sahayoniya ya ce, Shirin janyewar sojojin na Amurka bai zama abin mamaki ba,domin tun farkon rantsar da Donald Trump ne ya bayyana aniyarsa na janye sojojin kasar daga Syria.
HKI tana jin cewa, idan har Amurkan ta janye daga kasar Syria, to Turkiya za ta kara azamarta ta shimfida ikonta a cikin kasar.
Tun a Zangon shugabancinsa na farko ne dai Donald Trump ya bayyana cewa Idan kungiyar “Da’esh” ta kare,to kuwa kasarsa za ta janye sojojinta daga Syria.Daga baya kuma ya sanar da cewa janyewar sojojin za ta kasance ne sannu a hankali.
Ita kuwa ma’aikatar tsaron kasar ta Amurka ta sanar da cewa; An riga an rattaba hannu akan batun janyewar sojojin daga Syria.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Nemi Kasashen Duniya Su Taimaka Wa Libya Wajen Fita Daga Kangin Da Take Ciki
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp