“Waɗannan cibiyoyi ba iya Jigawa za su yi wa amfani ba, har ma da maƙwabta.

“Tare da sabbin na’urorin gwaje-gwaje irin su MRI da mammography, ba sai an je wasu jihohi domin samun irin waɗannan ayyuka ba,” in ji shi.

Gwamnan ya jaddada ƙudirinsa na ci gaba da inganta harkar kiwon lafiya a jihar, ta hanyar samar da sabbin ayyuka daidai da zamani.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamna Namadi Jigawa Kiwon Lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Tsohon Minista Ya Zargi Isra’ila Da Kasashen Yammacin Turai Da Kitsa Kashe-kashen Rayuka A Nijeriya 

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya. A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci. Hadin Gwiwar Kasashen Asiya Da Afirka Na Habaka Karfinsu Na Dogaro Da Kai Da Cin Moriya Tare Yaukaka Zumunci Da Makwabta A Aikace Tsakanin Sin Da Malaysiya “Suna shigowa su yanka mutanenmu, suna kashe Kirista da Musulmi, ’yan Arewa da ’yan Kudu,” inji shi. “Suna so su hargitsa kasar nan, kuma su bata sunan gwamnati, an taba kitsa irin hakan kuma har yanzu ana sake kitsa hakan.” Da yake zayyana makamancin haka, Fani-Kayode ya yi gargadin cewa, rikicin da ake fama da shi na da kamanceceniya da yadda aka kirkiri tashe-tashen hankula a zabukan shekarar 2015, inda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fuskanci irin wannan tashin hankali. “Haka aka shirya a shekarar 2014 kafin a kayar da Goodluck Jonathan, yanzu kuma sun fara shirin irin haka domin tunkarar 2027,” in ji shi. “Mun san su wane ne, kasashen waje daga cikin kasashen Yamma da Isra’ila da wasu da dama. Ba sa son kwanciyar hankali a Nijeriya.” Fani-Kayode ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da na tarayya da su kara daukar kwararan matakai. Ya bukaci gwamnatin jihar Filato da ta kara kaimi sosai sannan ya bukaci da a kara sa ido kan iyakokin Nijeriya. Ya karkare da sakon hadin kai da juriya da kishin kasa, “Nijeriya za ta ci gaba da wanzuwa, Nijeriya ba za ta fadi ba, za mu taka matsayi kan matsayi, kuma dimokuradiyyarmu za ta dore da nufin Allah, kuma mu tsaya a dunkule wuri daya. Allah ya tsare Nijeriya.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Ta Mallaki Tasoshin Fasahar 5G Miliyan 4.4 A Halin Yanzu
  • Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi
  • Tsohon Minista Ya Zargi Isra’ila Da Kasashen Yammacin Turai Da Kitsa Kashe-kashen Rayuka A Nijeriya 
  • An Yi Kira Ga Jihohi Da Su Kara Samar Da Ingantacciyar Hanyar Kiyon Lafiya
  • Cibiyar Nazarin Jinsi (CGS) Da Jami’ar Bayero Kano Za Su Yi Aiki Tare
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Garambawul A Fannin Kiwon Lafiya
  • Gwamnonin Nijeriya Sun Nuna Damuwarsu Kan Kashe-kashen Mutane A Filato 
  • Ina Da Ƙwarewar Da Zan Iya Zama Shugaban Ƙasar Nijeriya – Makinde
  • NNPP Ta Mutu, Kwankwaso Zai Sake Dawowa APC – Ganduje