Leadership News Hausa:
2025-04-19@00:30:42 GMT

Yaukaka Zumunci Da Makwabta A Aikace Tsakanin Sin Da Malaysiya

Published: 16th, April 2025 GMT

Yaukaka Zumunci Da Makwabta A Aikace Tsakanin Sin Da Malaysiya

Kasar Sin ta kuma nuna aniyarta ta lale marhabin ga shigar da karin kayan amfanin gona masu inganci na Malaysiya zuwa katafariyar kasuwarta inda ta kuma nemi kasar ta Malaysiya ta kara bai wa kamfanoninta kwarin gwiwar zuba jari a kasar.

 

Kasar Malaysiya ta san irin alheran da kamfanonin Sin suke ci gaba da kawo mata wajen raya tattalin arziki da ci gaban masana’antunta.

Wannan ya sa Sultan Ibrahim ya bayyana cewa, Malaysiya tana dora fifiko sosai a kan zumuncinta da kasar Sin, kuma za su ci gaba da yin aiki tare domin samun nasara ga kowane bangare, tare da kara matsa kaimi ga gina al’umma mai makoma ta bai-daya a karkashin ingantattun manyan tsare-tsare kuma a duk wani sauyi da za a iya samu a duniya.

 

Tabbas, Malaysiya tana shaida irin ci gaban da kamfanonin kasar Sin suke kawo mata. Babban jami’in kasuwanci na tashar teku ta Kuantan, Mazlim Husin, ya bayyana yadda yankin masana’antu na hadin gwiwar Sin da Malaysiya (MCKIP) ya bude sabon babi ga bunkasa ci gaban Kuantan tun bayan kaddamar da shi a shekarar 2013. Kafa kamfanin mulmula karafa na Alliance Steel ya kara wa sauran kamfanoni kwarin gwiwar bude rassansu a yankin masana’antun wanda ya habaka samar da ayyukan yi da walwalar al’ummar wurin.

 

Kasar Sin ta kasance kasar da ta fi kowace kasa zuba jari a Malaysiya, inda ko a bara ta zuba kimanin dala biliyan 6.4 a kasar wanda ya kai kaso 16 na kudin shigar da Malaysiya ke samu daga zuba jarin kasashen waje kuma ana sa ran ya samar da sabbin guraben ayyukan yi 20,000.

 

Kazalika, wani jami’in ofishin jakadancin Malaysiya mai kula da zuba jari dake Guangzhou, Safwan Nizar Johari ya tabbatar da cewa akwai karin kamfanonin Sin dake zuba jari a kasar musamman a bangaren motocin sabbin makamashi, wanda hakan na nuna zumunci mai kyau tsakanin Sin da makwabtanta.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Malaysiya ta a Malaysiya

এছাড়াও পড়ুন:

An Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Masu Jan Hankalin Xi Jinping” A Kasar Malaysia

 

Ya kara da cewa, CMG ta dade tana kasancewa ingantacciyar gada dake inganta fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, kuma ya yi imanin cewa, hadin gwiwarsu a wannan karo zai kara karfafa daddaden dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Pezeshkian: Hadin gwiwar Iran da Saudiyya zai zama abin koyi ga dukkanin kasashen yankin
  • Kare-karen Harajin Amurka “Dara Ta Ci Gida”
  • Majalisar Kasa Ta Rasha Ta Amince Da Yarjeniyar Dangantaka Ta Musamman Tsakanin Iran Da Kasar
  • Iraki Ce Zata Amfana Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka: Inji Sayyed Ammar Hakim
  • Najeriya da gwamnatin sojin Nijar da Nijar sun sasanta
  • Hadin Gwiwar Kasashen Asiya Da Afirka Na Habaka Karfinsu Na Dogaro Da Kai Da Cin Moriya Tare
  • Sin Da Vietnam Na Fitar Da Sabuwar Taswirar Zamanintar Da Al’Ummunsu Cikin Hadin Gwiwa
  • An Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Masu Jan Hankalin Xi Jinping” A Kasar Malaysia
  • UEFA: Mbappe Zai Jagoranci Real Madrid Yayin Da Ta Ke Fatan Kafa Sabon Tarihi A Santiago