KADGIS Za Ta Yi Amfani Da Sabuwar Manhajar Biyan Diyyar Filaye A Kaduna
Published: 16th, April 2025 GMT
Gwamna Uba Sani ya amince da sabon tsarin biyan diyya ta hanyar amfani da fasahar zamani ga Hukumar Kula da Bayanan Filaye ta Kaduna (KADGIS), da nufin dakile almundahana a harkokin biyan diyya na filaye a fadin jihar.
Daraktan Hukumar KADGIS Dr. Bashir Garba Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa (NUJ), rashen Rediyon Najeriya Kaduna, a ofishinsa da ke Kaduna.
Dr. Bashir Garba Ibrahim ya bayyana cewa wannan sabuwar manhaja za ta rika adana bayanan masu asalin filayen da za a biya diyya, da suka hada da daukar hoton ‘yan yatsun da lambar katinsu na dan kasa NIN, domin hana masu zamba karbar diyya akan filayen da ba nasu ba ne.
Haka zalika, Daraktan ya yi bayanin sauye-sauye da aka aiwatar a karkashin jagorancinsa tun bayan hawansa kan mukami.
Ya ce cikin shekaru biyu da suka gabata, KADGIS ta warware sama da kararrakin rikicin fili 700, tare da kaddamar da tsarin rangwamen kashi 20 bisa 100 ga wadanda suka biya dukkan bashin da ke kansu gaba daya, wanda hakan ya inganta samun kudaden shiga da inganta ayyuka matuka.
Dr. Bashir Garba ya tabbatar da cewa yanzu takardar mallakar fili (Certificate of Occupancy – C of O) tana cikin tsarin gaggawa, inda ake iya fitar da ita cikin sa’o’i 24 muddin dukkan sharudda sun cika, inda ake iya bayar da takardun shaidar mallakar sama da 200 a kowane mako.
A nasa jawabin, Shugaban NUJ reshen Rediyon Najeriya Kaduna, Umar Adamu S. Fada, ya yaba wa Daraktan da dukkan ma’aikatan hukumar bisa wadannan sauye-sauye, musamman na sabuwar manhajar biyan diyya, da kuma hanzarta fitar da takardun shaidar mallaka.
Ya nuna farin ciki da damar hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu, tare da bayyana shirin kungiyar na yin aiki tare da sashen hulda da jama’a na hukumar domin inganta samar da bayanai.
Kungiyar ta kuma yi tayin tallafawa hukumar, ta hanyar amfani da shirye-shiryen tasharsu don kara kusantar da jama’a ga ayyukan hukumar, da kara fadakar da su kan harkokin filaye a fadin jihar.
Umar S. Fada
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar EFCC Ta Kama Mutane 40 da Ake Zargi da Damfarar Intanet
Jami’an hukumar shiyyar Kaduna na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, sun kama wasu mutane arba’in da ake zargi da damfarar yanar gizo a kananan hukumomin Bida da Minna na jihar Neja.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar EFCC, Dele Oyewale ya raba wa manema labarai a Minna babban birnin jihar Neja.
A cewarsa an kama su ne biyo bayan sahihan bayanan sirri da ke alakanta su da ayyukan damfara na intanet.
Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da motoci uku, na’urorin samar da wutar lantarki guda takwas, na’urar sanyaya daki samfurin Hisense guda daya, na’urorin sarrafa wutar lantarki guda biyu, babura 10, kwamfutocin tafi da gidanka guda takwas, na’urar magana ta bluetooth hudu da wayoyin android 60 da dai sauran kayyaki.
Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.
PR ALIYU LAWAL.