‘Yan tawayen Sudan sun kafa tasu gwamnati
Published: 16th, April 2025 GMT
Yan tawaye a kasar Sudan sun sanar da kafa tasu gwamnati, bayan shekara biyu ana gwabza fada a kasar.
Shugaban rundinar kai daukin gaggawa ta (RSF), Mohamed Hamdan “Hemedti”, ya ce an kafa gwamnati a yankunan da kungiyarsa ke iko da su, musamman a yammacin Darfur.
Dagalo ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi a ranar Talata, inda ya ce, “A wannan ranar tunawa, muna alfahari da ayyana kafa gwamnatin zaman lafiya da hadin kai.
Ya kuma ce za a kafa majalisar shugaban kasa mai mambobi 15 da ke wakiltar dukkan yankunan Sudan.
Janar din wanda tuni Amurka ta kakabawa takunkumi bisa zarginsa da hannu a kisan kiyashin da aka yi a yankin Darfur, ya ce wasu kungiyoyi masu dauke da makamai kamar wani bangare na kungiyar ‘yantar da ‘yancin kai ta Sudan, sun shiga wannan gwamnatin.
Masana da daman a ganin wannan a matsayin koma baya ga duk wani yunkuri da ake na samar da zaman lafiya a wannan kasa.
Tun daga watan Afrilun 2023, ne fada tsakanin sojoji da dakarun kai daukin gaggawa na FSR ya barke lamarin da ya jefa kasar cikin rudani.
Akalla mutane 24,000 ne aka kashe, sannan Sama da mutane miliyan 13 ne suka rasa matsugunansu, ciki har da miliyan 4 da suka yi gudun hijira zuwa kasashe makwabta.
A kwanakin baya ne dai shugaban mulkin sojin na Sudan, Janar Al-Burhan, ya sanar da kwace iko da Khartoum babban birnin kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Mallaki Tasoshin Fasahar 5G Miliyan 4.4 A Halin Yanzu
Kazalika, Injiniya Xie ya kara da cewa, a cikin rubu’in farko na bana, sashen masana’antu na kasar Sin ya taka rawar gani wajen samun ci gaba ba tare da tangarda ba sakamakon ingantuwar tsari da zurfafa ayyuka wajen samar da sabbin ginshikan bunkasa ci gaba mai inganci. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp