Hamas ta bukaci hadin kan duniya domin kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza
Published: 16th, April 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira ga al’ummar duniya da su ba da himma wajen shiga wani gangami na tsawon mako guda domin ganin an kawo karshen mummunan yakin da Isra’ila ke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza da aka yi wa kawanya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, Hamas ta yi kira ga “kasashen Larabawa da na musulmi da kuma ‘yantattun mutane” na duniya da su halarci gangamin na ranakun Juma’a, Asabar da Lahadi (18, 19 da 20 ga Afrilu).
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta ayyana wadannan ranaku a matsayin “ranakun nuna fushin duniya dangane da mamaya.”
Hamas ta sake nanata bukatar daukar matakin gaggawa na kasa da kasa don kawo karshen “ci gaba da cin zarafi da kisan kiyashin da yahudawan sahyoniya suka yi wa al’ummar Falasdinawa a Gaza, wanda ke gudana a karkashin goyon bayan Amurka da kuma shiru na kasa da kasa.”
Har ila yau, ta yi kira da a gudanar da yajin aikin gama-gari a ranar Talata 22 ga watan Afrilu a dukkan jami’o’i da cibiyoyin ilimi na duniya domin tallafawa al’ummar Gaza da aka yi wa kawanya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Yi Aiki Tare Don Daidaita Mummunan Yanayi A Yankin Manyan Tabkuna Na Afirka
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron kwamitin sulhu na MDD game da yankin manyan tabkuna na Afirka a ranar 16 ga wata cewa, sakamakon ci gaba da kai hare-hare na kungiyar M23 a baya-bayan nan, ya ta’azzara yakin gabashin Kongo DRC, kuma daukacin yankin manyan tabkuna sun fada cikin rudani. Dole ne kasashen duniya su yi aiki tare kuma su hada kai don kawar da wannan mummunar yanayin cikin gaggawa.
Fu Cong ya jaddada cewa, dole ne a gaggauta tsagaita bude wuta domin hana shi ci gaba da ruruwa. Babu wata hanyar soji da za ta magance rikicin gabashin Kongo DRC, kuma tattaunawa ta siyasa ita ce kawai mafita. Dole ne kasashen duniya su dauki kwararan matakai don tallafa wa kasashen yankin manyan tabkuna wajen magance tushen matsalolin da ke haifar da gazawar shugabanci da rashin daidaituwar ci gaba a yankin. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp