Aminiya:
2025-04-19@01:10:03 GMT

Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas

Published: 16th, April 2025 GMT

Kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilan Nijeriya wanda aka ɗora wa alhakin kula da harkokin gudanar da mulki a Jihar Ribas, ya gayyaci gwamnan riƙon jihar, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar Wakilan, Akin Rotimi ya fitar a ranar Laraba.

An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato

Rotimi ya ce gayyatar na zuwa ne bayan ƙaddamar da kwamitin da Shugaban Majalisar Abbas Tajudeen ya yi a ranar Talata.

Ya ce gayyatar za ta bai wa kwamitin damar yin bita kan yadda al’amura ke gudana tun bayan kama ragamar aiki da Ibas ya yi a matsayin gwamnan riƙo a jihar ta Ribas.

Gayyatar wadda tuni ake aike da ita a hukumance, ta yi daidai da wasu tanade-tanade na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, inda ta buƙaci Ibas ya bayyana a gaban kwamitin da misalin ƙarfe 4 na maraicen ranar Alhamis, 17 ga watan Afrilun 2025.

A jiya Talata ce Majalisar Wakilan ta kafa tare da rantsar da kwamitin da zai kula da harkokin mulki a Jihar Ribas.

Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas ya ce kwamitin na wucin gadi mai mamba 21 zai yi aiki kai-tsaye da gwamnan riƙo “kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada.”

Majalisar ta kafa kwamatin ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya saka dokar ta-ɓaci wadda ta dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar saboda abin da ya kira “rushewar doka da oda.”

Har yanzu dai ’yan adawa na zargin cewa Tinubu ya kafa dokar ne saboda rikicin siyasar da gwamnan na jam’’yyar PDP mai adawa yake yi da Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ke ɗasawa da gwamnatin Tinubu ta APC.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Ribas Majalisar Wakilai Vice Admiral Ibok ete Ibas kwamitin da

এছাড়াও পড়ুন:

JAN KUNNE: Ɗan Atiku Abubakar ya mayar wa ɗan gwamnan Bauchi zazzafan martani

Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnna Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi.

Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya a zaɓen 2023.

A ranar Asabar ce, Shamsu ya ce Atiku ba ma ya tunanin zuwa ya nemi gafarar mahaifinsa duk kuwa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da yake yi.

“Bambancin da ake akwai yanzu shi ne Shamsu ya fito fili ya nuna mana cewa ka da mu sa ran samun goyon mahaifinsa (gwamnan Bauchi),” ya faɗa.

Ɗan Atiku Abubakar ya yi wannan martanin ne cikin wani saƙo da ya aiko wa da Premium Times a ranar Litinin, yana mai jaddada cewa gwamnan Bauchi ne ya yi wa mahifinsa zagon ƙasa a zaɓen 2023.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ya Yi Bikin Easter Tare da Al’ummomin Kiristoci
  • Dokar-ta-baci: Shugaban Majalisar Wakilai Ya Gargadi Kantoman Ribas
  • Rundunar ‘Yansanda Ta Tuhumi Jami’anta Da ‘Yan Kasar Sin Ke Raba Wa Kudi A Wani Bidiyo Da Ke Yawo
  • Kwamitin Gudanar da Kasuwa Maras Shinge Ta Maigatari Sun Ziyarci Fadar Gumel
  • Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Kidayar Jama’a Na Kasa
  • Majalisar Dokokin Zamfara Ta Dawo da Dan Majalisa Basko da Aka Dakatar
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Garambawul A Fannin Kiwon Lafiya
  • An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato
  • JAN KUNNE: Ɗan Atiku Abubakar ya mayar wa ɗan gwamnan Bauchi zazzafan martani