An Kashe Mutane 7 A Yayin Da ‘Yan Ta’adda Suka Ƙaddamar Da Wani Sabon Hari A Adamawa
Published: 16th, April 2025 GMT
An tabbatar da mutuwar mutane bakwai a wani sabon harin da ‘yan ta’adda suka kai a kauyen Garaha Lar da ke jihar Adamawa. Shugaban karamar hukumar Hong, Honarabul Usman Wa’aganda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa, wani mazaunin garin ya ɓata yayin da maharan suka lalata gidaje da kadarori.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An tsinci gawar mabaraci mai shekara 75 a Neja
An tsinci gawar wani tsoho mai suna Haruna Abdullahi mai shekara 75 daga garin Gumel na Jihar Jigawa a ƙofar babbar kasuwar Kure Ultra Modern Market da ke Minna a Jihar Neja.
Babu wanda zai iya cewa ga musabbabin mutuwarsa, amma ’yan kasuwa sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawarsa da safiyar ranar Juma’a a babbar ƙofar shiga kasuwar.
Ya kashe masoyin tsohuwar matarsa bayan sakinta a Neja PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – WikeKakakin rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin.
Ya ce, “A yau Juma’a 18/4/2025 da sanyin safiya, an tsinci gawar wani wanda aka bayyana sunansa da Haruna Abdullahi mai kimanin shekara 75 a ƙofar shiga kasuwar Kure.
“An ce mabaraci ne, kuma Bahaushe ne, ɗan jihar Gumel ne, kuma ba a ga wani alamar tashin hankali ba a jikinsa, an kai shi asibiti aka tabbatar da mutuwarsa.”